Abubakar Abba">

Cibiyar NAPRI Za Ta Kafa Wurin Kiwon Jakuna A Bauchi Da Ebonyi

Cibiyar Nazarin Kiwon Dabbobi ta kasa (NAPRI) da ke a garin Zariya cikin jihar Kaduna tare da hadin gwiwar kawayenta, suna aiki don kafa wuraren kiwon Jakuna yankin Toro da ke cikin Jihar Bauchi da kuma a jihar Ebonyi don kiyaye kiwon jakunan gida da bunkasa kiwon dabbobi.
Farfesa Abdullahi Mohammed, Babban Daraktan Hukumar ta NAPRI, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Zariya.
A cewar Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed cibiyar ta rattaba hannu yarjejeniyar fahimtar juna tare da kamfanin Earthwheel Logistics da kuma wasu abokan huda a wani lokaci a watan Fabrairu don kiwon sama da jakuna miliyan biyu a Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa 10 masu zuwa.
Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed, ya ce, ana sa ran jerin darajar za ta samar da dala biliyan biyu a duk shekara domin kasar, inda Mohammed ya kara da cewa, an yi hadin gwiwar ne da nufin inganta nau’in jakunan da za su kara wa shirin Gwamnatin Tarayya iri-iri na noma.
A cewar Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed, Majalisar Noma ta kasa, yayin taronta a Sakkwato ta lura cewa yawan jakuna a Nijeriya suna raguwa.
Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed, ya kara da cewa,“Bayan haka, Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta bayyana jakuna a matsayin nau’ikan da ke cikin hatsari saboda yawan dabbobin daga arewa zuwa kudu maso gabashin kasar don amfani da fitarwa”.
A cewar Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed, “Wani dalilin kuma da ya sa yawan jakunan su ke raguwa a irin wannan yanayi mai matukar tayar da hankali shi ne saboda ana amfani da fatun jakuna wajen maganin gargajiya a Asiya”.
A don hakan ne, Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed ya ce, Gwamnatin Tarayya ta bukaci cibiyar ta yi wani abu don inganta samar da jakuna, inda ya kara da cewa, tuni cibiyar ta samar da bangaren adana jakuna da kula da haihuwa.
Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed ya bayyana cewa, “A yanzu haka muna da jakuna sama da 100 a wannan bangaren. NAPRI, ta hannun wani abokin hadin gwiwa na kasar waje, ARLA Group da ke sarrafa madara, inda sun kulla yarjejeniya da al’ummar Fulani a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna don bunkasa samar da madara da lafiyar dabbobi.”
Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed, ya kara da cewa, hadin gwiwar ya dogara ne akan kafa makiyaya, inda ya cigaba da cewa, mun yi amfani da injunan gonarmu wajen noma wani babban filin kiwo a kewayen yankin Damau a karamar hukumar Kubau.
A cewar Babban Daraktan na Hukumar ta NAPRI, Farfesa Abdullahi Mohammed, wannan hadin gwiwar an yi shi ne domin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a yankin.
A wani labarin kuwa, wasu manoman Rani a garin Jos cikin jihar Filato sun bayyana cewa, ana sanun dimbin riba a fannin noman Tumatir a lokacin rani.
A cewar manoman wadanda suka fito daga sauran kananan hukumomin da ke jihar ta Filato, sun bayyana cewa, suna samun a kalla naira 100,000 kafin su koma gida.
Su na gudanar da sana’ar tasu ta noman Rani ce kamar a da Dam din Lamingo, inda suka shuka amfanin gona iri-iri, sun kuma kara da cewa, sun biya kudaden hayar gonakan da suka karba daga gun masu gonakan kafin suyi noman na Rani.
Yin noma a kusa da Dam, ya na yi wa manoman sauki sosai, inda su ke yin amfani da ruwan Dam din don yin ban ruwa ga amfanin gonakan da su ka shuka.
A cewar manoman na Rani, mutane da dama ba sa zuba kudade a fannin domin basu da kwarewa da kuma juriyar yi.
daya daga cikin manoman na Rani Mista Innocent Shehu wanda ya fito daga karamar hukumar Bokkos da ke a jihar ta Filato, ya sanar da cewa, shekaru biyu da su ka shige ya fara yin noman Rani don ya tallafawa kansa da kuma iyalansa.

Exit mobile version