Idris Umar" />

Cibiyar Nazarin Kimiyar Tsirrai Ta Kawo Wa Manoma Mashinan Aikin Gona

Exif_JPEG_420

A cikin satin da ya gabata ne cibiyar kimiyar tsirrai dake jami’ar Ahmadu Bello NAERSL tare da hadin guiwar ABUCOS sun gudanar da taron karawa juna sani da nunawa Kugiyoyin manoma 50 da suka fito da bangarori daban daban sabbin mashinan aikin gona na zamani da zai rage wahalhalun da ake fuskanta a wajan aikin gona.

Shugaban sashin Isar da dabarun noma Malam Murtaka Galadima, shi ya shugabanci taron.

A jawabinsa shugaban yace cibiyar tasu ta kawo wannan mashinane ga kungiyoyin manomanne don kawo ci gaban harkar noma a fadin kasa baki daya kuma yace, wannan hobasa, hadin guiwane tsakanin cibiyar da kamfanin cigaban jami’ar Ahmadu Bello Zariya ABUCOS .

Kuma ya tabbatar wa da manoma da cewa, wa’innan mashinan zasu taimakawa manoma sosai tare da kawo canJi a harkar cigaban noma kuma ya tabbatar da cewa zasu baiwa manomar damar mallakar mashina cikin sauki ba tare da samun wani tarnaki ba.

Shi ma mataimakin shugaban wannan cibiyar farfesa Ikanu Emmaniwel, da yazo a matsayin wakilin shugaban shugan cibiyar ya bayyanawa manema labarai cewa , samun mashinan noma da cibiyar ta kawo a yanzu bubban nasara ne saboda mashinane masu karamin jike da kasar India ta kera don yin aiki cikin sauki ba tare da shan wahalaba don haka yayi kira ga kungiyoyin manoman da suka sami daman halattar taron da suyi kokari wajan gwada wannan tsarin don samun ci gaban noma karshe yayi fatan Allah ya maida kowa gida lafiya.

Madam Asibi,daya daga cikin manoman mata da suka halacci taron ne a lokacin da take yiwa manema labarai bayani akan zuwanta wannan taro sai ta fara da godiya ga Allah da yasa suka zama manoma a wannan kasar tamu Nigeriya kuma ta kara da cewa in Allah yaso zasu jaraba wa’innan mashinan su gani don ga dukkan alama wahalar da suka sha a baya to a yanzu komi zai wuce tunda ga shi anzo masu da injin Caspa shinkafa ga na yin dashenta gana yankanta duk a karamin lokaci zaiyi maka aiki mai yawan gaske ba tare da samun damuwa ba don haka muna godiya.

Malam Muhammad shima wakilin wata kungiyarce daga karamar hukumar Giwa jihar Kaduna yace tuni sun shirya tsaf don karbar wannan tsari kuma sunyi matukar farin ciki da samunsa.

Daga cikin mashinan da cibiyar ta kawo akwai inji noma da huda dana casar shinkafa dana masara da dai sauransu anyi taro lafiya an tashi lafiya.

 

Exit mobile version