Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Cibiyar Rainon Ingila Ta Karrama Farfesa Abdalla Na Jami’ar NOUN

by
3 years ago
in LABARAI
2 min read
Cibiyar Rainon Ingila Ta Karrama Farfesa Abdalla Na Jami’ar NOUN
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Cibiyar Ilimi Ta Kasashen Rainon Ingila ta karrama Babban Mataimakin Shugaban Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), Farfesa Abdallah Uba Adamu, da digirin girmamawa, kamar yadda wata sanarwar manema labarai, wacce ke dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Jami’ar ta NOUN, Ibrahim Sheme, ta nuna.

Sanarwar ta cigaba da cewa: “Shugaban cibiyar, wanda mazaunin kasar Kanada ne, Farfesa Asha Kanwar, shi da kansa ne ya mika ma sa takardar shaidar girmamawar a lokacin biki na tara da cibiyar ke yi a dandalin wasanni na Murray Rugby Stadium a Edinburg da ke kasar Scotland.

Cibiyar ta gudanar da taron nata ne daga ranakun 9 zuwa 13 ga watan Satumba, 2019.

Labarai Masu Nasaba

Zargin Sauyin Sheka Yasa Majalisar Dokokin Kano Ta Dage Zamanta Na Ranar Litinin

Deborah: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bukaci A Zauna Lafiya

Taken taron na wannan shekarar shi ne ‘Innobation for Kuality Education and Lifelong Education’.”

Cibiyar ta himmantu ne wajen ganin bunkasa hanyoyin cigaban dan adam.

A ranar Litinin ne 9 ga watan Satumba a ka fara gudanar da bikin, inda Farfesa Adamu ya ke daya daga cikin mataimakan shugabannin jami’o’i uku wadanda a ka karrama, wadanda kuma su kadai ne su ka kasance ‘yan kwamitin cibiyar.

Sauran su ne, Farfesa Nageshwar Rao na budaddiyar jami’ar Indira Ghandi National Open Unibersity (IGNOU) da ke India da Dakta Caroline Seelig, shugabar kwalejin kimiya da fasaha wacce ita budaddiyar jami’a ce da ke kasar New Zealand.

Tsohon shugaban cibiyar ta COL, Sir John Daniel, ne ya ke shugabantar kwamitin.

Mahalarta taron sun yi maraba sosai da girmamawar da a ka yi wa Farfesa Abdallah Adamu bisa manyan nasarorin da ya samu na kirkiro fasahohi masu yawa a nahiyar ta Afrika, musamman abinda ya shafi samar da sana’o’i ga yara mata a tsawon shekaru uku da rabi da ya shafe a jami’ar ta NOUN.

Farfesa Adamu ya na daga cikin jagorori takwas fitattu a kan kirkiro da sabbin hanyoyin ilimi budaddu wadanda a ka karrama, kuma daya daga cikin ’yan Afrika biyu da a ka karrama da wannan fitacciyar karramawar a wajen taron.

Gudan, dan Afrikan da ya sami lambar yabon shi ne, Farfesa Mandla Makhanya, mataimakin shgaban budaddiyar jami’ar kasar Afrika ta kudu (UNISA).

Ita dai wannan lambar yabo ta ‘Honorary Fellow of the Commonwealth of Learning’ a na bayar da ita ne a bisa gagarumin gudunmawar da wani ya bayar ta fuskacin yin karatu a budaddiyar jami’a a sassa kamar na ayyukan wallafa da su ka hada da makaloli da jawabai da kuma koyarwa.

A kan kuma bayar da ita ne kadai ga ’yan asalin kasashen rainon Ingila, sannan ita kuma karramawa ce ta tsawon rai.

Cibiyar ta COL ta na ambata wadanda za ta karrama ne a lokacin tarukanta, ba ta kuma bukatar a gabatar ma ta da wasu sunayen ’yan takarar da za ta karrama, domin ita ce ta ke zabo su da kanta bisa cancantarsu, kamar yadda ta zabo Shehin Malamin Jami’a Abdalla.

Farfesa O. Jegede, wani tsohon mataimakin shugaban jami’ar ta NOUN, shi ma ya amshi wannan karramawar a shekarar 2013.

Like this:

Like Loading...
Tags: National Open University of NigeriaNOUNProf. Abdalla Uba Adamu
SendShareTweetShare
Previous Post

Bashin Nijeriya Ya Kai Naira Tiriliyan 24.39 A Shekara Daya

Next Post

A Barcelona Zan Yi Ritaya, Cewar Messi

Labarai Masu Nasaba

Zargin Sauyin Sheka Yasa Majalisar Dokokin Kano Ta Dage Zamanta Na Ranar Litinin

Zargin Sauyin Sheka Yasa Majalisar Dokokin Kano Ta Dage Zamanta Na Ranar Litinin

by
12 hours ago
0

...

Deborah: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bukaci A Zauna Lafiya

Deborah: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bukaci A Zauna Lafiya

by
15 hours ago
0

...

Ganduje Ya Umurci Bala Ya Kula Da Ofishin Shugaban Ma’aikata Fadar Gwamnatin Kano

Ganduje Ya Umurci Bala Ya Kula Da Ofishin Shugaban Ma’aikata Fadar Gwamnatin Kano

by
19 hours ago
0

...

Deborah: Matasan Musulmai Ba Su Kona Min Gidana Ba —Bishop Kukah

Deborah: Matasan Musulmai Ba Su Kona Min Gidana Ba —Bishop Kukah

by Abubakar Abba
22 hours ago
0

...

Next Post

A Barcelona Zan Yi Ritaya, Cewar Messi

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: