Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Cibiyar horar da matasa hanyoyin Inganta sana’u tare da Zama abubuwan amfani ga al’umma ta sha alwashin samar da Ingantancen horo domin samar da hanyoyin Inganta sana’a fadin Jihar Kano, jawabin haka ya fito daga bakin Jami’an tsare tsaren cibiyar Yuresa Alhaji Shu’aibu Hassan Alkanawi ne ya bayyana haka alokacin bikin bada lambar Karramawa ga Manajar Bankin Jaiz Dake Hotoro. A Jihar Kano.
Alkanawi yace akwai rashin fahimta cewar sojoji ko ‘yan sanda ake sa ran magance matsalar tsaro dake addabar kasar, ya ce, hanya mafi sauki itace cinye lokutan matasa ta hanyar shagaltar dasu kan sana’o’insu, domin sai mutun bashi da aikin yi ke sa matasa neman hanyar abin sawa a bakin salati. Amma idan matashi na da sana’a, yana jin kudi a aljihunsa, mai zai kai shi bata lokaci wajen ayyukan ta’addanci.
Saboda haka sai ya jinjinawa shugabar wannan Banki bisa kishin al’umma, musamman yadda ta aminta da hada hannu da wannan cibiyar domin samar da rancan kudi da takin zamani ga manoma. Yace mu kuma a karkashin wannan cibiyar muna zaunar da mutun mu koya masa yadda zai lura da abinda aka bashi, sannan kuma ya yi kyakkyawan amfani da abinda ya karba.
Yayin da take gabatar da jawabinta Manajar Bankin Jaiz shiyyar Hotoro, Hajiya Rahama Jibrin, ta bayyana aniyar Bankin Jaiz na hada hannu domin taimakawa Jama’ar Kano domin habaka harkokinsu na yau da kullum, ta ce bara kananan Hukumomin Jihar Kano uku muka shigar cikin wannan tsari, Amma Sakamakon nasarar da aka samu bana mun dinka wancan adadi.
A karshe Hajiya Rahama Jibrin ta ja hankalin wadanda suka amfana da karbar wannan bashi da suyi kokarin mayarwa da Banki kudin kansancewar kudin Jama’a ne, kuma ba dadi ace sai anyi amfani da ‘yan sanda wajen kokarin karbo basukan da aka bayar. Babu shakka muna alfahari da abokan mu’amalar Bankin Jaiz, musamman hadin kan da muke samu daga gare su.
Cikin wadanda aka Karrama akwai ita Manajar wannan Banki na Jaiz shiyyar Hotoro Hajiya Rahama Jibrin, Shugaban Majalisar Mahaddata Alkaur’ani Na Jihar Kano Goni Sunusi Abubakar, ma’aikata Bankin Jaiz reshen Hotoro da sauran mutanen da suke bai wa wannan cibiyar gudunmawa ako da yaushe.