Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandari ta kasa (NECO) a jiya Laraba ne ta sake sakamakon jarrabawar daliban da suka zana jarrabawa ta kammala sakandare (SSCE) da suka kammala a tsakanin watan Oktoba da Nuwamba, inda hukumar ta dauki tsattsauran mataki kan cibiyoyin da aka kama da satar jarrabawa.
Sakamakon jarabawar ya nuna cewa daga cikin dalibai 1,209,992 da suka zana jarabawar, dalibai 894,101 sun samu nasara da sakamako mai kyau ciki har da darasin Turanci da na Lissafi.
Bayanin fitar sakamakon, wanda ya fito ta hannun Rijistara da Babban Jami’imin gudanarwa (CEO) na hukumar NECO, Farfesa Godswill Obioma, ya nuna cewa sun samu kesa-kesan magudin jarabawa guda 33,470, yana mai karawa da cewa makaratun 12 ne wannan lamarin ya shafa tare da samun masu sanya ido 24 cikin lamarin.
Rijistaran ya bayyana cewar makarantun da aka samu da magudin jarabawa, an daina la’akari da su na tsawon shekara biyu, yayin da kuma jami’an sanya ido ‘Sufabaizos’ guda 24 da aka samu da hannu cikin lamarin an dakatar da su bisa samunsu da laifuka daban-daban da suka shafi magudi.
Shugaban ya kuma bayyana cewar sun shirya wani shiri na musamman da zai baiwa daliban da suka gaza samun damar zana jarabawarsu sakamakon zanga-zangar ENDSARS.
Obioma ya jero sunayen jihohin da matsalar jarabawa ya shafa sakamakon matsalar zanga-zangar EndSARS, sun kunshi Oyo, Osun, Ekiti, Legas, Edo, Ondo da kuma wasu cibiyoyin zana jarabawa a jihar Ribas, Abia, Enugu da babban birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, daga cikin dalibai 1,221,447 d asuka zana jarabawar, dalibai 665,830 maza ne, a yayin da kuma 555,617 suka kasance mata.