A yau za mu kalli sana’o’i kamar haka; Wanzanci, Fawa, Dori.
Wanzanci ita ce sana’ar da aka san Wanzamai da yin ta a jiya, sannan kuma ba a yi mata kutse waton hawan kawara. Wanzamai su ne a matsayin likitoci a wancan lokaci. Shin abin haka yake a yau? Mece ce sana’ar wanzanci? Wani masani mai suna Bashir Aliyu Sallau a Mukalarsa(2012:485) ya kawo mana’ar wanzanci a Hausance da cewa, ” tana nufin amfani da askar aski domin yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da koshiya don cire belun -wuya.” Sana’ar wanzanci ba ta tsaya nan ba don kuwa ana amfani da ‘yar tsaga don yin kaho da cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani. A sana’anar wanzanci dai ana yin hujen kunne da yanke ya tsan cindo, da yanke linzami a cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma masu yin sana’ar wanzanci na bayar da gudunmawar magungunan gargajiya ga wadanda suke bukata.
Masanin ya kara da cewa, sana’ar wanzanci ta tabo aikin likita a kasar Hausa kafin zuwan asibitin zamani. Dalili kuwa shi ne, wani daga cikin ayyukan wanzanci shi ne kula da lafiya musamman ta jarirai da kananan yara, ta wani fannin ma har da lafiyar manya. Masu yin ire-iren wadannan ayyuka ana kiran su wanzamai wadanda dole su kasance masu cikakkiyar lafiya, masu hankali da nutsuwa.
Su waye suka fi yin sana’ar wanzanci? A mafiyawancin maza ne suke yin sana’ar wanzanci, amma ana samun wasu mata wadanda saboda rashin wani namiji a gida ko kuma don wani dalili sukan koyi wannan sana’a daga mahaifinsu. Ana gadon wannan sana’a wajen kakanni na bangaren mahaifi.
Matsayin wannan sana’a a jiya. Kamar yadda muka ambata a baya, wanzamai su ne likitocin wanccan zamanin domin ba ya ga sana’arsu ta aski da shayi da cire anguraya da kaho sun bayar mahgunguna da duba yara da manya su ba su magani.
Baya ga haka, sana’a ce wadda ta ba wa al’ummar Hausawa ayyukan yi da madogar don samun kudin shiga da rufin asiri.
Sana’ar fawa, sana’a ce mahauta suke yi wanda ake kiran su da rinjawa. Fawa sana’a ce wadda ake sayen dabbobi a yanka don samar da nama ga al’umma. Mahauta suna sarrafa nama ta hanyoyi daban-daban wadanda suka hada da balangu da tsire da kilishi da dama wadanda suka hada da sayen dabbobi daga wurin wadanda suke yin kiwo da kuma sarrafa naman dabbobin danye ko gasasshe don sayarwa ga masu bukata. Wannan dalili ne ya sa wannan sana’a take cikin manyan sana’o’in gargajiya na Hausawa masu yin ta suka shahara, kuma ana yin fataucin naman da aka sarrafa musamman kilishi zuwa sassan da ke makwabtaka da kasar Hausa ta kusa da ta nesa.
Dori, sana’ar dori na daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausa da suka shahara a jiya wajen kula da lafiyar al’ummar kasar Hausa da ma makwabta, don kuwa a wancan zamani idan kashin mutum ya karye ko ya goce ko kuwa ya sami tarde a wata mahadar kashinsa idan aka kira masu yin dori za su dora shi ko su gyara wurin da rauni yake ya kuma warke cikin dan kankanin lokaci ba tare da fuskantar wata matsala ba. Wannan kuwa ya faru ne saboda wadanda suka gaji yin wannan sana’a wurin nasu mahaifan.
Zuwan Turawa ya samar da asibitocin kashi a kasar Hausa, wadanda suke duba da bayar da magunguna na matsalolin kashi da kuma dora karaya.
Da wannan za mu iya cewa, malam Bahaushe yana da likitan kashi tun kafin zuwan Turawa kasar Hausa, amma da yake ba sun zo ne don su gina mu ba, don su gina kansu suka zo, suka lalata namu ta hanyar yi mana zagon kasa, suka kafa nasu da inganta shi. Hakazalika, wannan sana’a ta dori ta samawar al’ummar Hausawa ayyukan yi abin dogaro.