Cikar Shekara 43 Na Sarkin Zazzau Shehu: Gidajen Malamai Da Suke Birnin Zariya Sun Yi Addu’o’i

Ranar takwas ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2018, rana ce da mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya cika shekara 43 da kasancewa Sarki a masarautar Zazzau, wato an nada shi sarki a ranar takwas ga watan Fabrairun shekara ta 1975 kenan.

Tun a safiyar Alhamis takwas ga watan fabrairu, duk inda ka duba abin da idonka ke nuna ma ka shi ne halifofin gidajen malamai na birnin Zariya da gidajen ne fiye da shekara dari uku suka yi suna tare da bayar da ilimi na ko wane fanni, suka kasance a fadar Zazzau, domin yin addu’o’I na ganin wannan rana da mai martaba Sarkin Zazzau ya cika shekara 43 da hawa karagar Zazzau.

Babban limamin Zazzau, Shekh Dalhat Kasim Yero shi fara addu’ar da aka tsara yi, inda ya farad a godiya ga mai kowa mai komi, na yadda ya sa mai mai martaba Sarkin Zazzau ya yi tsawon rai a`mulkin Zazzau, tare da yin jagoranci na adalci ga duk wani da ke masarautar Zazzau. Bai dakata ba, sai da ya yi addu’ar karin samun lafiya da karin hakuri da kuma hangen nesa da kowa ya san cewar, mai martaba Sarki na da su a tsawon mulkin da ya ke yi a masarautar Zazzau, daga shekara ta 1975 zuwa wannan shekara ta 2018 da mu ke ciki.

Sauran wadanda suka yi addu’o’I a lokacin wannan taro, sun hada da Na’ibin Zazzau da Sarkin Ladanan Zazzau da kuma limamin Kona na Zazzau da dai sauran Halifofin Gidajen malaman da suka sa Birnin Zazzau ta yi suna a idon duniya, ba a jihar Kaduna ko kuma arewacin Nijeriya, duniya baki daya Bayan an kammala addu’o’in da masarautar Zazzau ta tsara gudanarwa, sai kuma mai martaba Sarkin Zazzau ya gabatar da jawabinsa ga dinbin zazzagawa da suka halarci taron addu’o’in day a gudana a fadar zazzau.

Da farko mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya nuna matukar godiyarsa ga al’ummar masarautar Zazzau na yadda dare da kuma rana suna ba shi goyon baya da kuma addu’o’I in da ake yi ma sa daga lokacin da ya kasance sarkin Zazzau a shekara ta 1979 zuwa wannan shekara da mu ke ciki, wato shekara ta 2018.

A cewar mai martaba Sarkin Zazzau, duk ci gaban da ake cewar an samu a masarautar Zazzau, da kuma zaman lafiyar da aka samu a masarautar Zazzau, duk ba a same su ba, sai da duk wani da ke masarautar ya bayar da gudunmuwa ta bangarori da dama, kamar shawarwari da kuma addu’o’I da za a iya cewar su ne suka zama silar ci gaba da kuma zaman lafiyar da aka samu a masarautar Zazzau a shekara 43 da suka gabata.

A kan haka, sai mai martaba Sarki ya nuna matukar jin dadinsa na yadda tun a shekara ta 1975 da aka nada shi sarkin Zazzau, al’ummar masarautar Zazzau, sun dauki wannan sarauta da aka yi ma san a su ne, ya ce ya tabbatar da haka ne na soyayyar da ake ma sa ako wane lokaci, ba tare da gajiyawa ba.

A dai jawabin mai martaba Sarkin Zazzau, ya zayyano sunayen gwamnonin jihar Kaduna guda ashirin daga ya yi aiki da su, daga shekara ta 1975 zuwa wannan shekara ta 2018, sunayen gwamnonin sun hada da,

 1. Gwamna Abba kyari,
 2. Usman Jibrin,
 3. Mukhtar Mohammed,

4Ibrahim Mahmud Alfa,

 1. Abdulkadir Balarabe Musa,
 2. Abba Musa Rimi,

7Alhaji Lawal Kaita,

 1. Usman Mu’azu,
 2. Dan giwa Umar,
 3. Abdullahi Sarki Muktar,
 4. Abubakar Tanko Ayuba,
 5. Mohammed Dabo Lere,
 6. Lawal Jafaru Isa,
 7. Hameed Ali,
 8. Umar Faruf Ahmed,
 9. Ahmed Mohammed Makarfi,
 10. Mohammed Namadi Sambo,
 11. Patrict Ibrahim Yakowa,
 12. Mukhtar Ramalan Yero,

Sai kuma na ashirin da ke gwamna a jihar Kaduna a yau, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i.

Bayan ya kammala bayyana sunayen gwamnonin, sai mai martaba Sarki ya yi addu’a ga gwamnonin da suke raye na goyon bayan da suka ba shi a lokacin da suke mulki, su kuma wadanda suka koma ga mai duka, mai martaba Sarik ya yi ma su addu’a.

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ei-Rufa’I ya gabatar da jawabi a wajen addu’ar, inda da farko ya nuna matukar gamsuwarsa na yadda mai martaba sarki ke ba gwamnatinsa duk goyon bayan da suka dace, wanda a cewarsa dalilin da yasa ken an gwamnatinsa ta sami nasarorin da al’umma da dama ke furtawa.

Gwamna El-Rufa’I ya kammala da cewar, babu ko shakka, gudunmuwar mai martaba Sarkin Zazzau a fagen hanyoyin zaman lafiya, batun ya wuce masarautar Zazzau da jihar Kaduna, sai dai a yi batun Nijeriya baki daya, sai ya yi addu’ar karin lafiya ga mai martaba sarki domin ya sami dammar sauke nauyin da ke kansa.

Baya ga daukacin Hakiman masarautar Zazzau da suka halarci wajen addu’ar da aka yi, mai martaba Sarkin Keffi, Dokta Chindo Yamusa ya kasance a fadar Zazzau ga Wamban Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da ya wakilci mai martaba sarkin Kano, Malam Muhammadu Lamido Sunusi na biyu da kuma Sarkin Juwa da dai al’umma da suka fito daga sassa daban-daban

na ciki da wajen Nijeriya.

 

Exit mobile version