Shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote ya bayyana cewa, yawan asarar da kamfaninsa ya tafka ya kai na dala miliyan 900 a cikin kasuwan hannun jarin Nijeriya. shahararen dan kasuwan ya nuna cewa, kudadensa ya sauka kasa ne tun daga dala biliyan 18.4 zuwa dala biliyan 17.5 a ranar Alhamis na kasuwan hannun jarin, inda ya sauka a matsayin da yake a cikin masu daga matsayi na 106 zuwa matsayi na 114 a cikin masu girman arziki a duniya. Dangote dukiyarsa ta karu ne tun daga ranar 13 ga watan Disamba kusa da karshen shekarar 2020, daga dala 15.5 zuwa dala 17.8. Wanda ya samu rabar dala miliyan 600 a kwanaki bakai na shekarar 2021, amma sai ya tafka asara fiya da ribar da ya samu.
Shi dai farashin hannun jarin kamfanin Dangote Cement Plc wanda shi ne kamfani mafi girma a kasar nan kuma shi ne babban kamfani mai samar da siminti a kasashen Afirka ya rasa kashi 8.13,daga naira 244.90 a ranar Alhamis zuwa naira 225 a ranar Jumma’a. Dangote shi ne kadai dan Nijeriyan da ake lissafawa a cikin manyan masu kudi na duniya wanda ya kasance a cikin mutum 500, wanda kuma shi ne mutum na daya da ya fi kowa kudi a yankin Afirka.
“Mafi yawanci yana samun kashi 86 cikin arzikinsa daga kasuwancin siminti da kamfanin Dangote Cement ki gudanarwa. Yana da hannun jari kai tsaye a kamfanin ta karkashin kamdanin Dangote Industries.”
Mafi yawancin kadaranbsa ya hada har da takin zamani wanda yake samar da tan miliyan 2.8 a kowacce shekara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa ya bayyana.