Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Cikin Shekara Guda Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Cafke Miyagu 2,682

by Muhammad
December 28, 2020
in LABARAI
2 min read
Miyagu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

Daga ranar 1 ga watan Janairun 2020 zuwa yanzu Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta samu nasarar cafke mutum dubu biyu da xari shida da tamanin da biyu (2,682) bisa zargin aikata laifukan fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, fyaxe, sara-suka da sauran laifuka daban-daban a ciki da wajen jihar.

samndaads

A sanarwar da Kakakin Rundunar ‘yan sandan DSP Ahmed Muhammad Wakil ya fitar, ya shaida cewar an samu waxannan nasarorin ne a bisa qoqari da himmar kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Lawan Tanko Jimeta wanda ya tashi tsaye wajen ganin ya tsarkake jihar daga miyagun ayyuka.

A cikin shekara xayan, sun kuma ce sun samu nasarar kwato bindigogi da suka haxa da AK-47 guda (43); Dane Gun (28); SMG 3; Scorpion guda 1; Pump Action (3); Double Barrel Gun (4); Double Barrel Gun da AK-47 kirar gida; wata bindiga Single Barrel kirar gida guda 6; da kuma Fistol 12 kirar gida, sai kuma wasu Fistol xin guda 4 waxanda ba kirar gida ba.

DSP Wakil ya cigaba da jero nasarar cikin shekara da cewa sun kama motoci qira daban-daban guda 18; Babura 16.

Sai kuma dabbobi da suka samu nasarar kama sun haxa da Shanu 201; Tumaki guda 24; sai kuma Awaki 18.

DSP ya kuma ce, a cikin wannan watanni 12 xin sun kama kuxin da ya kai miliyan biyu da dubu xari biyar ta casa’in (2,590,000) lakadan; takardar kuxi 666 ‘yan dubu xaya-xaya da ake zargin na jabu ne; sai kuma takardar dala dubu xaya-xaya guda 28 da ake zargin na bogi ne.

Ya kuma qara da cewa sauran wasu qarin makamai da suka sun haxa da Adduna da Barandami 126; Wuqaqe 8; Sanduna guda 7; wasu kirar alburai; Layin waya guda 20; da sauran nau’inkan wuqaqe.

“Wasu kayakkain sata da aka kamo sun haxa da; wayoyin salula guda 16; Laptops guda 3; ATM na bankuna daban-daban guda 9; tayun ababen hawa; kayakkin kwalli da zobuna; wayoyin wutan lantarki masu tsayi sosai guda 22, da kuma mabuxan makallai na musamman; da sauran kayan mata da aka kama a cikin wannan lokacin,” in ji DSP Ahmed Wakil.

Daga nan rundunar ta tabbatar da cewa ta ja xamararta wajen ganin ta inganta aiki gami da daqile aikace-aikacen miyagu a sabuwar shekarar 2021 da za a shiga, don haka ne ma rundunar ta shawarci masu aikata laifuka da cewa su canza matsayarsu domin kuwa a shirye suke da su magance ayyukan ta’addanci a faxin jihar.

Kana Kwamishinan ‘yan sanda ya nemi haxin kan jama’an jihar ganin ya cimma manufofin kyautata tsaro a jihar da ma kewayenta.

SendShareTweetShare
Previous Post

Zanga-zangar EndSARS Ta Tabbatar Da Kasancewarmu Masu Son Zaman Lafiya –Sheikh Yahaya  

Next Post

Kirsimeti: Ku Cigaba Da Jajircewa A Fagen Daga – Shugaban NAF Ga Jami’ansa

RelatedPosts

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

by Yahuzajere
40 mins ago
0

A kokarinta na tabbatar da tsaron iyakokin kasar nan, Hukumar...

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

by Daurawa Daurawa
3 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya Rahotonnin da suke fitowa daga fadar...

Tattabaru

Abin DaYa Sa Tattabarun Da Buhari Ya Saki Ba Su Tashi Ba – Adesina

by Muhammad
4 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa...

Next Post
Jami'ansa

Kirsimeti: Ku Cigaba Da Jajircewa A Fagen Daga – Shugaban NAF Ga Jami’ansa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version