- Sun Ceto Mutane 67
- ’Yan Daba Fiye Da Dubu Uku Sun Shiga Hannu
- An Kwato Taliyar Dangote Ta Tallafin Korona Katon 1,958 Da A Ka Waske
Daga Nasir S. Gwangwazo
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama masu garkuwa da mutane har guda 117, sannan ta yi nasarar ceto rayukan mutane guda 67 da a ka kama ko a ka tsare ko a ka yi yunkurin safararsu ba bisa ka’ida ba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP. Habu Sani, a lokacin da ya ke bayani kan cikarsa shekara a kan mukamin Kwamishian ’Yan Sanda na jihar, inda ya kara da cewa, ko a lokacin bayar da tallafin Korona daga masu hannu da shuni mai taken CA-COBID-19, sai da jami’ansa su ka kwato katon din taliyar da attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya bayar da sunan tallafa wa marasa karfi, amma wasu marasa tausayi da jinkai su ka waske da kayan zuwa wani waje daban.
Bugu da kari, an yi ta samun koke-koke kan yawaitar ayyukan ’Yan Daba a Birnin Kano, wadanda hatta jami’an tsaro su kan yi fargabar arangama da su a wancan lokaci. To, amma a cikin shekara guda kacal da zuwan CP. Sani jihar, al’amura sun yi matukar sauyawa.
Kan hakan ya bayyana irin matakan da su ka dauka wajen shawo kan matsalar, ya na mai nuni da cewa, babban abinda ya fi mayar da hankali a kai tun zuwansa jihar shi ne, tsari na ‘Community Policing’, wanda ya ke bayar da dama a hada hannu tsakanin jami’an ’yan sanda da kuma al’ummar gari wajen shawo kan kowacce irin matsalar tsaro da ke addabar al’umma.
Bisa wannan kokari ne rundunar ta kafa kwamitocin ‘Community Policing’ a matakai na jiha, kananan hukumomi da yankunan manyan ofisoshin ’yan sanda na shiyya.
Matakai daban-daban da kwamishinan ya dauka na kwarewa da dabarun aiki ne su ka kai ga iya ceto rayukan mutane 67, wadanda su ka hada da 28 da a ka sace, 10 wadanda a ka yi garkuwa da su, hudu wadanda a ka killace da kuma 25 wadanda a ka yi safararsu.
Baya ga damke masu garkuwa 117, an kuma kama ’yan fashi 215, ’yan damfara 86, dillalan kwayoyi 67, ’yan daba 3,130, barayin shanu 21 da na mota 75, Adaidaita 34, babura 53 da barayin kekuna guda takwas.
Kwamishina Habu Sani ya gode wa Babban Sufeton ’Yan Sandan kasar, IGP Adamu, bisa dora shi bisa tafarki da ya ke yi ta hanyar koyar da shi masaniya da makamar aiki tare da umarni mai kyau, don kai wa ga wadannan nasarori.
Idan dai za a iya tunawa, daya daga manyan abubuwan da a ke yaba wa jagorancin rundunar ’yan sanda a Kano shi ne, yadda ta tafiyar da lamarin dokar zaman gida ta Korona, musamman a lokacin azumin Ramadana na 2020, inda a ka fara lafiya, a ka gama lafiya ba tare da tashin hautsini a ko’ina a cikin fadin jihar ba.