Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
Hukumar yaki da ayyukan fasa kwauri ta Nijeriya (Nigeria Customs Serbice) reshen jihohin Adamawa da Taraba, ta tara sama da Naira miliyan dari daya da goma sha daya (111,000,000.00), a matsayin kudaden haraji cikin watanni bakwai.
Shugaban hukumar a jihohin biyu Mista Adetoye Francis, ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Yola, ya ce, duk da matsalar ayukan ‘yan ta’adda da lalacewar hanyoyi da karyewar gadoji da su ke haifar da koma baya wajan samun kudaden shigar.
Mista Adetoye yace, wata matsalar da jami’an hukumar ke fuskanta itace ta rashin samun hadinkan jama’a mazauna kan iyakokin jihohin biyu da Jamhoriyar Kamaru.Ya ce, amma hukumar ta tara kudaden da kame wasu jarkokin man fetur dari hudu.“Duk da wadannan matsalolin mun tara wadannan kudaden harajin Naira 11,745,317,43 mun kuma tara wasu kudaden Naira miliyan arba’in da biyu da dubu dari bakwai da hamsin da shida na tarar shigo da motoci ta haramtacciyar hanya.”
Mista Francis ya koka da cewa a wasu lokutan jami’an hukumar kan gamu da fushin jama’a wanda hakan ke kai su ga kokarin sha da kyar da taimakon sarakunan gargajiya a yankin kan iyakar jihohin biyu da jamhoriyar Kamaru.Baya ga kudaden shigar da hukumar tatara shugaban ya kuma mika hukumar tsaron farin kaya ta Cibildefiance jarakun man fetur 400 ta da kame kan iayakokin jihohin biyun da Kamaru.