Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, muna gode masa muna neman taimakonsa, muna neman agajinsa, muna neman tsari daga gare shi, wanda Allah Ta’ala ya kaddara ma sa bata baka samun wani makusanci ko masoyi balantana mai agazawa da zai agaza ma sa ya shiryar da shi, mun yadda cewa babu abin cancanta da bauta sai Allah, shi kadai ba shi da abokin tarayya. Mun kuma yadda cewa Annabi Muhammadu (SAW) dan aiken Allah ne, kuma cikamakin annabawa, Allah ne ya aiko shi da shiriya, da addinin gaskiya domin ya dora shi a kan addinai ko da a ce kafirai da munafukai da algungumai da marasa gaskiya basu so haka ba.
‘Yan uwa akwai wani abu da ya zama kamar tsutsa a cikin al’umma, yana ta cutar da su, amma kuma da yawa mutane ba su damu da waiwaya wa kan wannan abin ba, gidaje da dama sun wargaje saboda an samu fushi a gidan, aure da dama ya mutu saboda fushi, iyaye da dama sun rabu da ya’yansu, makota sun yi rigima da makotansu abin har yana kai wa da a samu wata abila da wata kabila suna rigima, ko masu sana’a da wata sana’a suna rikici, ko wani bangare na kasa yana rikici da wasu kabilu na wani bangare.
dauki misalin abin da yake faruwa da Fulani a wani bangare babban misalin shi ne, menene yake kawo wannan abu, shi ne fushi.
Ayau za mu yi kokari mu duba muhimmancin tsare fushi, domin fushi na farko dai dabi’a ce ta dan’Adam amma biye masa shi ne matsala, don in ka lura da fishi wani yanayi ne na zuciyar dan’Adam, wanda ke sa jini ya dinga gudana da karfi a jikin dan’Adam zuciya ta dinga bugawa da sauri. Allah ya halicce shi ne a jikin dan’Adam, da zai yi amfani da shi wajen tare abin da yake tsoro, ko kuma magance abin da zai cutar da shi, ko kuma kokarin canja yananyin da bai dace ba. Wani abin mamaki dangane da wannan shi ne iya tare fushin ka iya magance fushinka yana daya daga cikin abububwan da ke bai wa dan’Adam karfi ta bangaren uku.
1.Farko ta bangaren lafiyar jikinsa, dumi idan fushi ya taso maka sai ka bi ye masa kai ta yi, idan aka je aka auna jikin sai a gaya haura, ka ga idan ka fiye murmushi da farin ciki ba za a je a gwada jininka a ce ya haura ba. Masana ma sun ce yawan murmushi da farin cikin yana maganin hawan jinni, to amma kai kullum a cikin fushi, to wai kai me ya faru ne, wannan duniyar kwana nawa za a yi cikin da zaka zauna kai kullum a cikin fushi haba Malam ai gara ka yi dariya, amma ga talauci ga kasha-kashe ga fushi, to wane zaka ji da shi.
2.Ta bangare na biyu da tsare fushinka zai taimaka maka, shi ne zai baka karfin cin nasara a kan makiyankan idai ka iya tsare fushinka ya zama baka yin fushi a inda bai kamata fushinka ya bayyana ba, sannan uwa uba zai baka karfin samun kusanci zuwa ga Allah domin shi Allah mai tausayi ne mai rahama ne, idan ka duba Al’kur’ani ko wacce sura cikin surori (114) daya ce kawai ba a fara ta da Bisimillah ba, kuma ko wacce Bismillah me take cewa; ‘Da sunan Allah mai rahma mai jin kai’. Amma rahamar nan ta Allah jin kan nan na Allah ya kan ware shi ga wasu mutane, ba duka rahamar da zamu samu a wajen Allah ba iri daya za mu samu ba, wani ya fi kusa da rahamar Allah, kuma abin mamakin shi ne, Allah Tabaraka wata’ala ya kamantu da wannan rahama kamar yadda ya fada cikin sura ta 59 Aya ta 23 shi mai rahama ne mai jin kai ne.
Amma in kana so ka kai ga samun rahamar Allah cikin saukin akwai wasu kamannin da ya kamata ka kamantu da su, Allah zai maka rahama, Allah yai mana rahama, da ni da ku, har ma da wanda bai ce amin ba. Allah tabaraka wata’ala ya ce “Ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga wajen Ubangiji, da samun Aljanna, wanda fadin wannan Aljannar, fadin sammai da kassai ne, amma sai aka ce kar ka tafi da sanyin jiki, ka tafi da sauri ma’ana ku yi rige-rige shiga Aljanna, ita kuma wannan Aljannar an tanadar da ita ne ga masu takawa, wajen bayyana su wanene masu takawa, Allah bai barka ka tsaya kana dogon tunani ba sai ya ambaci su wanene masu takawa.
Allah ya kamanta maka su na farko ya ce wadanda suke kashe kudi suke ba da kudi a lokacin farin ciki da lokacin bakin ciki, ta hanyar da Allah ya amince, kasan matsalar kudi kamar yadda kake da dokokin a kan hanyar da za ka bi ka samo kudi haka kake da doka a kan hanyar da zaka bi ka kashe kudi.
Dukiya ta Allah ce saboda haka bai yadda ka neme ta ta hanyar da bai amince ba kawai don an ce maka zo ka tsare wa mutane dukiyarsu sai ka yi ta diba, kuma ranar juma’a ka zo masallaci ka yi ta muzurai, wannan ai sai a Nijeriya, an baka tsaron dukiyar al’umma kuma ka zo masallaci kana muzurai, to da wanne za mu ji, da kwashe mana kudi ko da muzurai, alagarfarta Malam ai gara ka yi murmushi ko ma rage zafi, ka fahimta, to don haka neman kudin akwai ka’ida kashe kudin ma akwai ka’ida, su bayin Allah suna kashe kudin a cikin ka’idar, ko ana cikin wadata ko ana walwala su kan duba inda ya dace su ba da, shi ne Allah ya baka kamar shi ta daya shi ne ba su da rowa.
Kuma da masu hadiye fushi, wato fushi al’adace dabia ce, kowa yana da shi, akwai inda ba ka yi fushi ba, akwai inda in baka yi fushi ba ka saba wa Allah. Mutum kawai ya zo gidan sa ya samu wani kato yana…, ah alagafarta Malam, kuma sai ya yi dariya ai wurin dariya bane, ka same kato a kwance a kan gadonka da matarka kuma ka ce wai kai baka fushi, ala gafarta Malam kuma ka samu wani yana wanka wa babarka mari, kuma ka ce wai mu bama fushi, ba kwa fushi, ai in ka ce baka fushi ai sai babar taka ta tsine maka, ka fahimta, fushi dabi’a ce, amma hadiye shi bin Allah, idan ya taso sai ka yi abin da ya da ce, yanayin da ake ciki a kasarmu Nijeriya yanayin yin fushi ne.
Misali, garkuwa da mutane, da satar shanun mutane, da kashe mutane wannan ai abin bakin ciki ne, amma bai kamata kuma a ce wai duk wanda ya yi fulatanci ya zama dan ta’adda ba, sai muce a nemo masu laifi a hukunta su, amma idan muka yi fushi muka ce a kori Fulani a ci mutumcin Fulani wannan fushin bai dai dai ba, saboda fulatanci yare ne, saboda cikin Fulani akwai Maube, akwai wanda yake Gonga ne, akwai modibbo cikin fulani, akwai Malami akwai kai har shugaban kasa ma akwai Bafulatani to kawai don wasu Fulani sun yi laifi sai a ce a kori Fulani masu kirkin in an yi haka an hadiye fushin, a’a ba’a hadiye fushi ba.
To mun ji dadi da aka ce an yayyafawa kurar ruwa a inda ta taso don a zauna lafiya, ka san wannan satin labaran suna da dan dadi-dadi, ana cewa wasu sojojin an sara musu su je su huta, wadansu kuma su zo a gwada su.
To su wadanda za a gwada din mu yi mu su addu’a, Allah ya sa su samu nasara, Allah ya sa a daina kasha-kashe a Nijeriya, Allah ya sa a daina garkuwa da mutane, Allah ya sa kada su ce sai sun nade kayan mutane, ka san wani yanzu zai ce tunda an nada shi to sai ya nade, to kuma kai a nada ka ka nade kayan mutane, ai ka ga bai yiwu ba, to kai da aka nada ka ka yi kokari ka ci nasara ka tafi gida ko da da ‘yan kudi kadan ne, Allah ya sa mu dace, saboda haka su mutanen kwarai bayin Allah din nan wadan da za su samu aljanna din nan ta hanyar da zaka iya hadiye fushi shine ka yafe wa wanda ya yi maka ba dai dai ba yafiya ana yin ta a kowane mataki, daga daga sama ya yafe wa na kasa, na kasa ya yafe wa na sama, kai har a gwamnatance a yin yafiya ba shi ne ake kira Amnesty ba, tunda an yi Amnesty a can kwanar me ya sa ba za a yi wa fulani ba, tunda ana yin irin wannan yafiyar, to ai ya kamata suma Fulani a ce su ajiye makami a ce su zo a yafe musu, suma su daina kashe mutane yafiya tana da kyau, sai ya ce yana son masu kyautatawa.
Su kuma mutanen kwarai ba wai wadanda basa yin laifi bane, aa sai a zo a cikin masallaci sai kaga kamar ka zama wani mala’ika mala’ika nan ko kafin ka shigo masallacin ko ka manta ne, saboda Allah kafin kazo masallaci baka dan… jiya ne ko shekaran jiya kadai yi tunani, kai dai ka gane, allah dai ya yafe mana, kada kazoo masallaci kace wai kai ma’ilaka ne ka, aa ina mutum ne kai, Allah ya yafe mana.
Cigaba a gobe in sha Allahu.