Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar Afrika, Ahmad Ahmad na tsawon shekara 5 bayan samunsa da laifukan almundahanar kudade da kuma karbar rashawa.
Cikin sanarwar da FIFA ta fitar a ranar Litinin, hukumar ta ce Ahmad Ahmad dan kasar Madagascar zai kuma biya tarar dala dubu 220, baya ga haramcin na shiga harkokin gudanarwar wasannin na Afrika har tsawon shekara biyar.
Tun a Maris din shekarar 2017 ne Ahmad Ahmad ya yi nasarar darewa kujerar shugabancin hukumar ta CAF ya yinda kuma a halin yanzu yake neman wa’adi na biyu a shekarar 2021.
A cewar FIFA Ahmad Ahmad ya yi mata zamba cikin amince ta yadda ya ci amanar hanyar da ta kai shi kujerar shugabancin ta hanyar karbar nagoro da kuma azurta kansa da kudaden kula da harkokin kwallon kafar Nahiyar.
Ko a cikin watan Afrilun bara, tsohon jami’in hukumar ta CAF MR Fahmy ya aikewa FIFA wasikar da ke zargin Ahmad Ahmad da karkatar da wasu kudaden karbar rashawa da kuma cin zarafi da muzgunawa jami’in hukumar musamman mata, matakin da ya kai ga kameshi watanni biyu bayan zargin yayin gasar kwallon kafar mata da ta gudana a kasar Faransa amma kuma aka sakeshi kwana guda bayan kamen.
Dama dai bukatar Ahmad Ahmad ta ci gaba da jagorancin CAF ya gamu da kakkausar suka daga shugaban hukumar kwallon kafar Senegal Augustine Senghor, ya yinda shugaban hukumar kwallon kafar Mauritania Ahmed Yahya da Jackues Anouma na Ibory Coast kana attajirin Afrika ta kudu Patrice Motsepe dukkanninsu suka nuna bukatar tsayawa takara don neman kujerar.