Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa cin kwallaye da dama yana da mutukar amfani saboda yadda ba’a samun damar bayar da maki da yawa a tsakanin kungiyoyin da suke neman lashe gasar firimiyar Ingila ta bana.
Solkjaer ya bayyana haka ne bayan da kungiyar sa ta Manchester United ta sake kafa tarihi a gasar firimiyar Ingila bayan ta zazzaga kwallaye 9-0 a ragar kungiyar Southampton a ranar Talata, abin da ya ba ta damar yin kan-kan-kan da Manchester City a saman teburin gasar da maki 44 kafin Manchester City ta buga wasanta a jiya.
Ko a kakar wasannin da ta gabata, sai da Southampton tayi irin wannan rashin nasara da kwallaye 9-0 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Leicester City a filin wasa na St. Mary wanda hakan yasa kenan cikin shekara biyu aka yiwa kungiyar ta Southampton wannan zazzagar.
Manchester United ta taba kafa irin wannan tarihin na zura kwallaye 9-0 a ragar kungiyar Ipswich Town a lokacin tsohon mai koyar da kungiyar Sir Aled Ferguson a shekarar 1995, ya yin da ta sake maimatawa a bana a lokacin Ole Gunner Solkjaer.
Solkjaer ya ce yana bukatar yaransa da su jaddada jajircewarsu wadda za ta kai su ga dage kofin gasar a bana wanda kuma a cewarsa hakan ba zai faru ba idan har ‘yan wasan basu dage ba sun nuna jajircewa da sadaukarwa.
“Cin kwallaye da dama a wannan kakar yana da mutukar muhimmanci idan muka kalli yadda ba’a bayar da tazarar maki da yawa a tsakanin kungiyoyin da suke neman lashe gasar firimiyar bana” in ji Solkjaer
Ya kara da cewa “Dole ne mu sake da gewa da cin kwallaye a kowanne wasa domin hakan zai iya taiamakawa wajen lashe gasar domin kowa a yasan a shekarar 2012 tazarar kwallaye ce tasa bamu lashe gasar firimiyar ba”
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sha kashi a hannun kungiyar Wolberhampton Wanderes da ci 2-1 kuma a karo na farko kenan cikin wasanni tara da Wolbes ke samun nasara a gasar ta firimiyar Ingila.
Arsenal ta karkare fafatawar ta ranar Talata ne tare da ‘yan wasa 9 bayan alkalin wasa ya bada jan-kati ga David Luis da kuma mai tsaron ragarta wato Bernd Leno wanda shima a daidai minti na 75 aka sallame shi daga fili.