Daga Abubakar Abba, Kaduna
Kwamishinar mata da walwalar jama’a ta Jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba, ta yi gargadin cewar, nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta fara hukunta iyayen da ke yin watsi da ‘ya’yan su da kuma cin zarafin su.
Hafasat a hirar ta da kafar dillancin labarai ta kasa jiya Alhamis a Kaduna ta ce, dokar baiwa yara kariya ta bayar da damar sanyawa irin wadannan iyayen takunkumi a kan cin zarafin ‘ya’yansu.
Ta yi nuni da cewa, mafi yawanci iyaye suna yin watsi da harkar ‘ya’yansu, inda hakan ke jefa yaran cikin hadurra iri-iri na rayuwa.
Acewar Hafsat, amfanin dokar itace don a rage yawan karuwar cin zarafin yara da wasu iyayen suke yi a jihar, inda dokar ta tani takunkumi ga dukkan iyayen da suke cin zarafin yayan su.
Kwamishiniyar taci gaba da cewa, “idan muka gano iyayen da suke yin watsi da ‘ya’yan su, dokar za ta hau kansu.”
Hafsat ta kuma koka akan yadda wasu iyayen suke cin zarafin ‘yayan su da kansu. Ta bayyana cewar a kwanan baya ma’aikatar ta ta samu korafi akan wani uba da ya yiwa ‘yar shekar bakwai dukan tsiya har ta samu raunuka. Akan safarar yara kuwa Hafsat tace, ma’aikatar tana bibiyar shari’a guda shida a Kotu.