CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Cinikayyar Sin Da Ketare Ta Yanar Gizo Ta Yi Matukar Bunkasa A Bana

by CRI Hausa
December 28, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Cinikayyar Sin Da Ketare Ta Yanar Gizo Ta Yi Matukar Bunkasa A Bana
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Biyo bayan jerin matakan da hukumomin kasar Sin ke cigaba da dauka domin bunkasa fannin tattalin arziki da hada hadar cinikayya a cikin gida da kuma ketare, alamu sun tabbatar da cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu. Ko shakka babu, wadannan matakan sun taka gagarumar rawa wajen bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasar Sin da sauran sassa na duniya. Alal misali, rahotanni daga lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin na cewa, lardin wanda ke matsayin cibiyar hada-hadar cinikayyar waje a gabashin kasar, ya samu bunkasar cinikayyar ketare ta yanar gizo cikin watanni 11 na farkon wannan shekarar.

Yawan hajojin da aka fitar ketare daga lardin ta cinikayyar yanar gizo tsakanin wannan watanni 11 sun kai na kudin Sin yuan biliyan 91.16 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 13.95, adadin da ya karu da kaso 28.9 cikin dari a shekara guda, kamar yadda sashen lura da cinikayyar lardin ya bayyana. Bugu da kari, adadin hajojin sayayyar daidaikun mutane da aka yi cinikayyar su tsakanin lardin da kasashen ketare ta yanar gizo, sun karu da kaso 33.4 bisa dari, inda darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 33.9, wanda hakan ya haifarwa lardin karuwar makin hajojin da ake shigarwa da kaso 1.2 bisa dari. Yanzu haka dai lardin Zhejiang, ya kafa sabbin cikakkun yankunan gwaji na cinikayyar hajojin da ake fitarwa ketare har guda 7, wadanda suka hada da na Wenzhou, da Shaoxing, da Huzhou, da Jiaxing. Sauran su ne na Quzhou, da Taizhou da kuma Lishui.
Mahukuntan lardin dai na kira ga kananan hukumomin da aikin ya shafa da su tsara dabarun tallafawa manufar. A cewar daraktan sashen lura da cinikayyar waje ta lardin Sheng Qiuping, mahukuntan lardin na Zhejiang sun sha alwashin samar da karin kyakkyawan yanayi, da ingantattun hidimomi, na bunkasa hada hadar cinikayyar waje ta yanar gizo. Lallai wannan alamari ya kasance wani labari mai faranta rai ga kasar Sin da kasa da kasa musamman a wannan halin da ake ciki na karayar tattalin arzikin duniya a sanadiyyar barkewar annobar COVID-19. (Ahmad Fagam)

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Kasar Sin Tana Kokarin Yin Kirkire-kirkire A Cikin Yanayin Bude Kofa

Next Post

Messi Bai Karya Tarihin Pele Ba, Cewar Santos

RelatedPosts

Wane Irin Tsarin Cudanyar Tattalin Arzikin Duniya Ake Bukata?

Wane Irin Tsarin Cudanyar Tattalin Arzikin Duniya Ake Bukata?

by CRI Hausa
17 hours ago
0

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, wasu mutane sun...

Xi Ya Saurari Rahoton Aikin Gwamnatin Yankunan Hong Kong Da Macao

Xi Ya Saurari Rahoton Aikin Gwamnatin Yankunan Hong Kong Da Macao

by CRI Hausa
17 hours ago
0

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya saurari...

Jiangxi: An Taimakawa Mutane Wajen Saukaka Begen Gida Da Suke Yi Ta Kafar Bidiyo Kai Tsaye

Jiangxi: An Taimakawa Mutane Wajen Saukaka Begen Gida Da Suke Yi Ta Kafar Bidiyo Kai Tsaye

by CRI Hausa
17 hours ago
0

A kauyen Huikeng a garin Xinwan na gundumar Xiushui a...

Next Post
Santos

Messi Bai Karya Tarihin Pele Ba, Cewar Santos

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version