Abba Ibrahim Wada" />

Cinikin Hazard: Chelsea Da Real Madrid Sun Amince A Kan Fam Miliyan 88

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta amince zata siyar da dan wasanta na gaba, Edin Hazard, ga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid akan kudi fam miliyan 88 da kuma karin wasu kudaden idan har dan wasan yayi kokari a kasar ta Sipaniya kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Tun da farko dai Chelsea ta bukaci Real Madrid ta biya fam miliyan 130 farashin da Madrid din taga yayi mata tsada saboda dan wasan kwantiragin shekara daya kawai yake dashi a Chelsea hakan yasa aka dinga kai ruwa rana kafin daga bisani kuma a cimma matsaya.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea babu tabbacin ko zata iya siyan wani dan wasan wanda zai maye mata gurbinsa bayan da tuni hukumar kwallon kafa ta duniya ta dakatar da kungiyar daga siyan ‘yan wasa bayan an kamata da laifin siyan kananan ‘yan wasa ba bisa ka’ida ba.

Tun bayan da aka kammala gasar cin kofin Europa da Chelsea ta doke Arsenal a wasan karshe a birnin Baku dake kasar Azerbaijan dan wasa Hazard, wanda ya cilla kwallaye biyu a raga ya bayyana cewa ya buga wasansa na karshe a kungiyar.

Sabon kociyan Real Madrid, Zinadine Zidane dai shine ya bayyana cewa zai siyi manyan ‘yan wasa domin tun karar kakar wasa ta gaba sakamakon rashin buga abin kirki a kakar wasan data gabata wanda hakan yasa akayi waje da kungiyar da wuri a gasar cin kofin zakarun turai sannan kuma ta kammala gasar laliga a mataki na uku maki 19 tsakaninta da Barcelona wadda ta lashe gasar ta bana.

Tuni dai Real Madrid ta siyi dan wasan baya Elder Militao daga kungiyar kwallon kafa ta FC Porto dake kasar Portugal sannan kuma a satinnan ta siyi dan wasa Luca Jobic, dan kasar Serbia, daga Frankfurt ta kasar Jamus.

Exit mobile version