Bisa sakon da ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta fitar, a shekarun baya-bayan nan, an ci gaba da samun sabuwar habakar hadin gwiwar tattalin arziki a yankin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO. Haka nan, cinikin kayayyaki ya dade yana kara habaka. A farkon rabin shekarar bana, yawan cinikin kayayyaki tsakanin Sin da sauran kasashe mambobin SCO ya kai dalar Amurka biliyan 247.7, wanda ya karu da kashi 0.8 bisa dari bisa makamancin lokaci na bara.
A sa’i daya kuma, hadin gwiwar zuba jari da tattalin arziki da fasahohi ya karu cikin kwanciyar hankali. Ya zuwa watan Yunin bana, jarin da Sin ta zuba kai-tsaye ga sauran kasashen mambobin SCO a dukkan sana’o’i ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 40, kana ayyukan zuba jari sun fadada a hankali daga fannonin da aka saba hulda a cikinsu kamar makamashi da ma’adanai, karafa da sinadarai, da gina manyan ababen more rayuwa zuwa fagage masu tasowa kamar tattalin arzikin fasahar zamani da kuma samar da ci gaba mara gurbata muhalli.(Safiyah Ma)