Cinikin Ketare Na Sin Ya Karu Da Kashi 22.2 A Watanni 10 Na Shekarar Nan

Daga CRI Hausa,

Alkaluman da hukumomi suka fidda a yau Lahadi ya nuna cewa, jimillar hada-hadar kasuwancin shigi da fici na kasar Sin ya karu da kashi 22.2 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara inda ya kai yuan triliyan 31.67 kwatankwacin dala triliyan 4.89 a watanni 10 na farkon wannan shekara ta 2021.

A cewar babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, adadin ya karu da kaso 23.4 idan an kwatanta da na shekarar 2019 gabanin barkewar annobar COVID-19.

Duka bangarorin biyu na shigi da fice, sun ninka adadinsu a watanni 10 farko na wannan shekara, inda suka karu da kashi 22.5 da kuma kashi 21.8 bisa 100 idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.

Alkaluman sun nuna cewa, a watan Oktoba kadai, adadin shigi da ficin kasar Sin ya karu da kashi 17.8 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, sai dai ya ragu da kashi 5.6 idan an kwatanta da na watan Satumba. (Ahmad Fagam)

Exit mobile version