Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Ciwon Basur Da Yadda Za A Magance Shi (1)

by
3 years ago
in MAGUNGUNA A MUSULUNCI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A uzubillahi minasshaidanirrajim Bismillahirrahmanirrahim. Wassalatu wassalamu ala rasulalillah wa’alihi wasahbihi wa man walahu. Bayan haka jama’a ina yi maku sallama irin ta addinin Musulunci Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’alah wabarakatuhu, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri namu mai albarka da yake bayanin cuktuttka da magungunansu, da kuma kariya wato ‘Wukaya’ a cikin koyar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama.

A yau insha Allahu muna so za mu yi magana ce wato akan Basur, ko kuma ‘Bawaaseer’ a Larabce kenan, ko kuma Basur, domin sunan ya samo asali ne daga kalmar Larabci, tun da kalmarmu ta Hausa tana cuduwa da larabci matuka. Shi Basur ciwo ne da yake faruwa a dubura ta mutum wato inda bayan gari yake fita. Wato shi nau’i biyu ne akwai khaariji akwai kuma daakhili, da kuma wanda yake yin tsiro domin shi wannan tsiro din shi ne Basur, da zai dan fito kamar kurji gefen inda bayan gari yake fitowa.

To shi wanna tsiro din akwai na ciki shi ne daakhili, akwai na waje shi ne khaariji. Shi na waje ya fi sauki wanda zai bayyana a waje, wano lokaci a ganshi ya bayyana wani lokaci kuma a ga ya bace, kuma in ya fara fitowa to shike nan kuma dimun da’iman kuma ya rika fitowa kenan. Wani lokaci ya rika yi wa mutum ciwo, wani lokaci kuma ya zamto baya ciwo.

Labarai Masu Nasaba

Abin Da Ya Kamata A Sani Game Da Zazzabin Beraye (Lassa Fever)

Bayani A Kan Ciwon Olsa (Ulser) Da Yadda Za A Shawo Kanta (2)

Shi kuma daakhili na ciki, shi ma tsiron yake amma a ciki, a waje za a bakin duburar lafiya kalau ba matsala, amma yana a ciki yayi wannan tsiron, to wannan shi ya fi hadari, kuma ya fi illa matuka kwarai da gaske. Ya kan yi ruwa wani lokaci a jiinsa, wani lokaci kuma ya kan huro jini a jikinsa. Shi girma-girma ne, kuma sannan mu kula, shi Basur yana da banbanci da fitar bayan gari, akwai wanda zai je bayan gari sai ya samu duburarsa tana zazzagowa, shi wannan ba Basur ba ne, mu gane wannan.

Insha Allahu za mu bisu daki-daki mu yi bayanin iri-irin cututtuka da suke faruwa a dubura, wadanda gaba daya kudin goro ake yi musu a ce musu Basir, ba duka ne Basur ba wannan mai fito da da kurji a gefen dubura shi kadai ne Basur ko ta ciki ko ta waje.

To dalilan da suke haifar da shi Basur suna da dama, akwai wanda haifuwa sakamakon jini, wanda yake assauda’a shi ne jinin mutum ya yi baki saboda rinjayar sanyi da bushewa, in aka samu rinjayar sanyi da bushewa sai jinin mutm ya rika gurbacewa, mutane sun kasu daban-daban, akwai wanda jikin yake kasancewa yana da rinjayar zafi da danyantaka, akwai kuma wanda da rijayar sanyi da bushewa, akwai wanda yake kasacewa da sanyi da danyantaka wato radabun kenan. To wanda yake da rijayar sanyi da bushewa, shi ake kira da ‘Assaudawi’ wato mutum yana matsalar baki a cikin jininsa.

Domin za ta iya kasancewa mutum dabi’arsa shi Sadawi ne amma bai samu rijaya ba mai bushewa ne a jininsa haka Allah ya yi shi, amma kuma bai samu rinjaya ba jikinsa yana nan dai-dai, don haka bai da wata matsalar fata bai da matsalar Basur, domin in aka samu wata rijaya to sai ka ga wasu cutuka suna bayyana, kamar su waswasi, da yawan bacin rai, kamar zargi da wasu abubuwa, ko kuma ka ga an samu shi Basur din, to daya daga cikin hanyoyin kenan.

Na biyu akwai gubacewar ciki sakamakon mutun yana cin wasu abubuwa da basu dace ba, ko yana yawan cika cikinsa fiye da kima, ko yana cin abubuwa masu tauri, kamar irinsu naman sa mai tauri ko na rakumi, ko dai wasu abubuwa masu gurbata ciki, ka ji ciki yana ta kugi yana fitar da iska da wasu abubuwa, to irin wannan ka sani cewa shi ma zai iya haifar da Basur.

Basur ciwo ne mai hadari matuka, idan har ya bayyana ba a daki mataki akansa ba, mun san akwai wadanda lamarin ya kan kaiwa ga yi masu aiki ‘Operation’ an yanka duburar tasu da wuka jini ya zuba an yi masu ayyuka, ka ga duk abin da zai ga a ce an tsaga jikin mutum a nan wuri da yake tattare da jijiyoyi dubunnai, wani a sakamakon haka za ka gaya samu raunin gaba kenan, domin shi asalin Basur din ma ya kan haifar da raunin gaba. saboda wannan tsiron da yake fita a mazaunin jijiyoyi ne, saboda jijiyoyin wannan wurin ba su da karfi ba su da kwari, to duk za su zama suna cikin rashin lafiya saboda bayyanar wannan Basur din. To sai ka ga mutum yana samun raunin gaba da wasu matsaloli a tattare da iyalinsa, sannan ya kan rage karfin gaba, baya ga haka ya kan rage girman gaban namiji, don jijiyoyin sun tattare wuri guda, wanda kuma ana so su zama a sake ba a takure ba, sai ka ga duk iya kokarin mutum na ya kai wani lokaci a wurin tarayya da matarsa sai ka ga baya iya kaiwa sakamakon wannan Basur din.

Kuma ya kan haifar da zubar jini daga dubura idan ya fashe, domin zubar jini daga dubura wannan maganarsa daban wannan ba a sa shi a layin Basur in sha Allahu shi ma nan gaba za mu yi bayaninsa, amma shi Basur din mai wannan tsiron in ya yi tsanani ya kunbura, to wani sai ka ga ya fashe, yadda muka ce akwai wanda za ka ga ruwa ne a jikinsa, akwai wanda kuma jini ne a jikinsa, idan jini ne za a ga jini yana lalata wa mutum wando, idan kumace ce yana lalata mata zani, in kuma ruwa ne zaka ga shi ma yana zuba wato mugunya kenan.

Saboda hadarin Basur ne ma har Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama akarkashin koyarwarsa mai kyau mai tsafta mai inganci, yake yi mana wani bayani cikin wani hadisi na Abuddarda’i Allah ya kara yarda da shi, ya ce lallai da da akwai wasu ‘ya’yan marmari da zan ce daga aljanna yake da zan ce maku ‘Atteen’ ne wato ‘Baure’ Manzon Asallallahu alaihi wasallama ya ce, lallai cinsa yana magance cutar ‘Bawaaseer’ wato Basur, yana kawar da cutar Basur, mun san cewa komai yana da maganinsa.

Shi ne masana suke bayanin cewa, akwai hanyoyi da ake bi a sarrafa Bauren nan a ci shi ya yi maganin Basur, idan har Basur ya riga ya haifu to kaga cin sa zai zama yayi maganinsa zai hana zama ya haifu a cikin ciki. Amma wannan tsiron da ya fito sai an yi amfani da wani magani da zai zamo ya motse shi ya kau da shi ko ta halin yaya ne, in dai aka samu maganin da za a shafa shi ko a cusa shi ya kasance da na ciki da na waje ya kanasance ya bushe, wato cin wancan baure ya kawar da shi, to bi iznillahi sai ka ga an samu dawwamammiyar lafiya. Idan kuma bai riga ya haifu ba kuma mutum yana amfani da wannan bauren to in sha Allahu za ka ga mutum ba zai kamu da cutar Basur ba, a karkashin koyarwa ta Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama. To jama’a a nan zamu dakata sai kuma mako zuwa idan Allah ya kaimu za mu dora daga in da muka tsaya. Muna rokon Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya, wassalamu alaikum warahmatullahi ta’alah wabarakatuhu.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Illar Rashin Yarda A Tsakanin Ma’aurata

Next Post

Daga Littafin Bakar Guguwa (5)

Labarai Masu Nasaba

Kwalara, Sankarau, ‘Lassa Fever’ Sun Kashe ‘Yan Nijeriya 156 A 2019 — NCDC

Abin Da Ya Kamata A Sani Game Da Zazzabin Beraye (Lassa Fever)

by
2 years ago
0

...

Bayani A Kan Ciwon Olsa (Ulser) Da Yadda Za A Shawo Kanta (2)

by
3 years ago
0

...

Bayani A Kan Ciwon Olsa (Ulser) Da Yadda Za A Shawo Kanta

by
3 years ago
0

...

Rigakafin Cututtuka A Saukake

Rigakafin Cututtuka A Saukake

by
3 years ago
0

...

Next Post

Daga Littafin Bakar Guguwa (5)

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: