Abubakar Abba" />

Ciwon Daji: Gwamnatin Tarayya Za Ta Bude Asusu Don Kula Da Masu Fama Da Larurar

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, nan ba da jimawa  za ta bude wani asusu na musaman don kula da masu fama da cutar daji a cikin Nijeriya.

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanireya sanar  haka ne a taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya a a kasar nan  da ya gudana a  Abuja.

Taron, wanda ya dada Cibiyar PACFaH@Scale, gidauniyyar Pink Blue da kungiyar  Gwamnonin Nijeriya  ne suka hada shi kuma an yi masa  taken ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a ji za su iya takawa domin inganta fannin kiwon lafiyar a Nijeriya.

Matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar Nijeriya da samar da hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakaya samu kiwon lafiya na gari sannan cikin farashi mai sauki na daga cikin batutuwan da ake tattauna a taron.

Ministan ya ci gaba da cewa,  gwamnati za ta kafa wannan asusu ne don taimakawa masu fama da cutar bayan kokawar da wata mata mai suna Serah Shimenenge dake dauke da cutar ta yi kan kaluballen da ta ke fama da su.

A cewar Serah, masu fama da wannan cuta a Nijeriya  na matukar shan tsadar magani, kama gada yin gwaji da kuma siyan magungunan da ya kamata su dinga sha akai-akai, inda ta kara da cewa, muna kokarin ganin cewa asibitoci masu zaman kansu sun bude wani bangare domin kula da mutanen dake fama da cutar kyauta.

Ministan ya kuma yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin dake haddasa wannan cuta cewa yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar, inda ya zayuana cewa,  hanyoyi sun hada da guje wa shan giya, shan taba sannan da shakar hayakin sigari.

Ya ce gwamnati ta dauki wasu matakan da za su taimaka wajen wayar da kan mutane game da cutar domin rage yawan mace-macen mutane a Nijeriya.

Idan ba a manta ba a watan Fabrairu ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta rawaito cewa mutane 116,000 na dauke da wannan cutar wanda daga ciki mutane 41,000 suka rasu inda kuma a yanzu haka cutar na daya daga cikin cututtukan dake kisan mutane a kasar nan harda  duniya.

Bincike ya nuna cewa karancin ma’aikata, tsadan farashin magani da gwaji na cikin matsalolin da masu dauke da wannan cuta ke mutuwa a kasar nan.

Har ila yau, duk  da haka gwamnati ta yi iya kokarinta domin ganin tra samar wa manya-manyan asibitocin gwamnati na’urorin gwaji na zamani,inda a yanzu haka kasar nan na da na’urorin gwajin cutar guda takwas a asibitoci daban daban.

Exit mobile version