Idris Aliyu Daudawa" />

Ciwon Kai Da Kuma Hanyoyin Magance Shi

Ciwon kan da ake kira da migraine, cikin harshen Turanci, wani ciwon kai ne mai tsaninin gaske da ke kawo rashin jin dadi kamar su tashin zuciya da kuma jin jiri. Wannan kalma ta migraine abin ya  samo asali ne daga harshen Faransanci wato daga kalmar ‘megrim’ wadda ma’anarta ke nufin matsaloli irin su jiri da tashin zuciya, da kuma ciwon kai. A dalilin wannan ma’anar ce a yau aka samo wannan kalmar ta migraine wadda kuma ake kiran ta da duk wadda ke dauke da ita ‘migraineur’.

Masana sun yi imanin cewar wannan cuta ta migraine na faruwa ne a sanadiyar wani abu da ke aukuwa da mutum a waje, wato outside trigger ke nan a Turance. Maufa,wato faruwar wani al’amari ne yake jawo shi. Idan abin ya faru sai abinnan da ke sa mutum ya ji zafi a cikin kwakwalwa ya faru. Wannan zafi na kwakwalwa shi yake haifar da tsukewar hanyar jini. Idan hanyar jinin ta tsuke sai mutum ya fada cikin wannan hali na ciwon kai mai tsanani na migraine.

Wannan ciwon kan na migraine kan faru ne cikin dan karamin lokaci daga baya kuma sai ya warke. Wani lokaci kuma yana daukar lokaci mai tsawo sosai. Idan ya dade abin baya da dadi ko kadan. Duk mai fama da da migraine zai gaskanta ita wannan maganar haka ne take.

Duk da tsananin na rashin dadi da kuma yawaitar wannan ciwon kai a tsakanin mutane, amma masana kiwon lafiya basu da ilimi mai yawa game da shi. Sai baya-bayanan da masu bincike a fannin lafiya suka fara gano asalin dalilan kamuwa da shi, sai kuma alamomin shi da kuma hanyoyi da za a bi don magance shi.

Yana kuma da muhimmanci a sani wannan matsala ya fi yawa ga mata. Amma tsananin shi ya danganta ne daga wannan mutum zuwa wancan mutumin.

Abubuwan da ke sanadiyar kamuwa da migraine

A wani binciken da masana suka yi game da shi ciwon kan na migraine, sun gano cewar wannan ciwon kan na faruwa ne a lokacin da hanyar jini a cikin kwakwalwa ya bude. Duk da cewar masana ilimin kimiyyar basu tabbatar da lallai cewar wannan shine makasudin abinda ke haifar da ita wannan cuta ba ta ciwon kan, amma lallai akwai sheda mai karfi wadda kuma ta nuna cewar dalililai irin su  na gado ne ko kuma   muhalli  suna daga cikin abubuwan,  da suke zama musabbabin ciwon kai na migraine. Ana sa ran cewa yayin da aka samu cigaban kimiyya ke bunkasa, haka nan ma dalilan kamuwa da ciwon za su rika kasancewa, hakanan kuma su magungunan su za su karu da kuma  ingantuwar su zata karu matuka gaya.

Kamar dai yadda al’amarin ya kasance wanda kuma yake nuna cewar, shi wannan ciwon kan ana gadon shi sosai. Idan daya daga cikin iyaye yana fama da wannan cutar,to akwai tunanin da yake nuna cewar kashi 50 cikin 100 da shima zai yi fama da cutar ta migraine  a rayuwar sa. Sanin kowa ne dalilan da suke jawo ciwon kan migraine al’amarin shi ma ya danganta ne daga mutum zuwa mutum.

Wasu daga cikin abubuwan da ke kasancewa sanadiyar kamuwa da ciwon kan

1.    Abinci: An tabbatar da cewar  abincin da mutum yake ci yana zama sanadiyar kamuwa da ciwon kai. Abinci irin su giya, da cakulet, kayan madara , wake, da irin su naman gwangwani wanda ya kunshi sinadarin nitrates. Wasu karin nau’oin abincin sun hada da kamar su soy sauce, sai kuma sinadarin caffeine, da aspartame da duk wani abincin da ake jika shi ko busar da shi, dukkanin su suna iya haifar da ciwon kan migraine.

2.     

Dalilai na wurin da ake zama ko muhalli : Wajen zama ma na iya taimakawa wajen samar da ciwon kan. Kamar wuta mai haske ko kuma wadda take walkiya, da hasken rana, da kamshi ko kuma wari mai karfi, da hayaki, da kuma  fenti da dai sauransusu wadanda ke faruwa a wurin da mutum yake zama.

3. Wasu sinadarai ne da jikin Dan adam ke samarwa: Pre-menstrual syndrome wato yanayin nan na rashin jin dadi wanda mata ke fama da shi lokacin dfa suke yin al’ada, na haddasa ciwon migraine. Maganin kwaya da ke hana daukan ciki shima na haddasa wannan ciwon kan.  wani jinya ne da matan da suka manyanta kanyi don dawo da kuzarinsu na kuruciya – shima yana kawo wannan ciwon kan.

4. Yanayi na rashin natsuwa: Rashin samun natsuwa wala Allah a gida ne ko kuma a wajen aiki ne yana daga cikin dalilan da ke kawo ciwon kan migraine.

5. Dalilai na canjin yanayin mutum : Abubuwa kamar canji yadda mutum ke samun bacci ko sauyi wajen motsa jiki ko kuma ciwon baya ko na wuya su ma kan haddasa wannan ciwon kan.

6. Sauyin yanayi: Canji yanayi shima wani abu ne da ke kawo ciwon kai sosai musamman lokacin zafi da kuma lokacin hunturu wato sanyi.

Alamun ciwon kan migraine

Abu mafi muhimmanci da ya kamata a sani game da migraine shine kowa da yadda yake jinsa ma’ana irin ciwon da zafin da ake ji sun danganta daga mutum zuwa mutum. Kamar yadda muka fada a baya dalilan da ke kawo shi sun banbanta haka zalika alamunsa.

Akwai alamu da dama da ake danganta su da wannan ciwon kan na migraine shi yasa wani lokacin ba a iya ga no lallai ciwon kan da ke damun mutum migraine ne. Amma dai yawancin abinda aka sani shi ne idan ciwon kan migraine zai fara yakan fara da abinnan da ake kira magrine aura.  Aura wani haske ne mai kamar walkiya ko kuma ganin gizo-gizo ko wata yana-yana hakan nan kafin wannan ciwon kan ya fara damuwar mutum. Bayan mutum ya kamu da ciwon kai na, migraine na iya sa tashin zuciya harma ya kai ga yin amai kamar yadda aka yi bayani a baya. Bugu da kari kuma babin ciki na iya  nuna su alamun migraine, shi yasa ma yawancin lokuta ya kan sa mara lafiya  yin amai.

Da akwai lokutan da alamun migraine basu bayyanuwa a fili a har gane su. Abin lura anan shi ne kada ko da wasa a daudi migraine da wasa domin wani lokacin yakan kai ga shanyewar gabobi abinda ake nufi da stroke.  Amma dai ita wannan cutar sau da yawa wani lokaci ba ta kaiwa ga matsala wadda take kasancewa mummuna ga mutumin daya kamu da ita cutar. Wani lokacin ma migraine yana nuna ga wata matsala ta rashin lafiya wacce take ta daban. Ko ma dai mine ne duk lokacin da mutum ya kamu da rashinn lafiya yakamata ya yi hanzari yaje asibiti, saboda ya samu ganin Likita.

Maganin cutar kai ta migraine

Hanyar da ake bi don magance cutar kan migraine sun hada da cin nau’in abinci wadanda suka kunshi Bitamin B12 bitamins na rage yawan da kuma karfi shi wannan ciwon kan nesa ba kusa ba. Wasu hanyoyin da ake bi don maganin wannan matsalar a gida sun hada da kula da cin  nau’oin abinci masu kyau, kuma ba masu haddasa ciwon kan ba. A rage cin abinci irin su cakulet, da jar giya, da caffeine da kuma tsohon cheese saboda ire-iren wadannan abincin suna daga cikin abinda ke iya haddasa ciwon kan.

BayananSannan kuma saka kankara a dai-dai wajen da kan ke ciwo na taimakawa sosai wajen rage radadin wannan ciwon kan. Kazalika kuma ko tausar jiki wannan shima yana taimakawa kwarai da gaske. Tausar wurin a hankali yana taimakawa hanyar jini da ke wurin sakewa ya  rika gudana ba tare da tangarda ba, da kuma samarwa ainihin  wurin natsuwa  sosai. Tausar kuma tana taimakawa wajen rage damuwa da kuma tashin zuciya da wani lokaci ke tare da wannan ciwon kan. Wani lokacin kuma za a samu natsuwa, a wuri mai duhu wanda ba a kwaranniya, na taimakawa sosai wajen  sauwakawa mutum ciwon kan migraine.

Kamar kullum ana kara jan hankali makarantanmu da a duk lokacin da mutum ya fuskanci wani rashin lafiya to ya yi kokarin ganin likita domin a tabbatar da ainihin matsalar cutar da ke damun shi.

Exit mobile version