Connect with us

KIWON LAFIYA

Ciwon Sanyi Da Alamominsa

Published

on

Idan masu karatu suna biye da mu, har yanzu muna nan cikin bayani kan ciwon sanyi da alamun kamuwa da shi, da irin illolin da yake tsakanin maza da mata, da dalilan da suke jawo shi. Kuma mun tsaya ne a kan illar da yake yi wa mace mai ciki da kuma yadda yake cin naman jariri tun yana cikin mahaifiyarsa. Za mu ci gaba.

Kuma kazanta da rashin kyakkyawan abinci yana kara wa ciwon karfi, ya kan kara tsanani in ya hadu da ciwon (Siflis) sai ka ga har da kurarraji, da ganin farin ruwa da gurbataccen ruwa, inda wani lokacin wani lokacin ya kan fara da ‘yan kuaraje, ko kurji daya a kasan ciki ko saman mara, ko tsakanin cinyoyi a gaba, wani lokaci kuma ko a hannaye ko a kafafuwa, wadanda suke da saurin jini wurin tabawa ko sosawa.

Banbancin su da na (Siflis) shi ne, su suna da zafi ko kaikayi in dai sun fito.

Sannan  sun fi saurin bayyana a jikin namiji fiye da mace, kurajen ke nan.

Shi wannan ciwon sanyin in aka kamu da shi, ana fara ganin alamarsa tun daga kwana uku zuwa sati biyu a mafi yawa, kuma ana iya warkewa gaba daya in aka samu maganinsa mai kyau. Sannan ya watsu sosai cikin duniya, da yake dama tsohon ciwo ne, musamman kasar Indiya da makotansu kamar yadda kididdiga ta nuna, ha rake cewa kashi 31 cikin dari na ciwon sanyi yana kasar Indiya.

Wannan wani nau’in ciwon sanyi kamar yadda ma’abocin littafin (Kissatul’adibba)  ya fadakar wanda yake sananne a fannin likitanci, da masu bincike, wanda shi dan kasar Indiya ne, ya kawo labarin wani mutum da ya kasance a nahiyarsu yake cewa, shi irin wannan ciwon mai rarake cikin jiki ya cinye shi, ya kama mutumin.

Shi ko mutum ne da kwata-kwata bay a iya hakuri da jima’i, sanda alamar ciwon ta bayyana, sai da likitoci suka ce masa ya kauracewa saduwa amma sai ya ki ji, saboda haka wata rana yana saduwa da matarsa, sai kawai gabansa ya guntule a cikinta. Nan da nan suka garzaya wurin wani likita akan wannan matsala, inda ya tambaye su tun yaushe ciwon yake jikinsu? Sai wannan ya ce, tun shekara 13, ya ce to ba a ba su magani tare? Ya ce ana ba su. Likita ya ce, to me ya sa ciwon ya ki warkewa tun wancan lokacin? To ku gaya min gaskiyar rayuwarku, domin matsala ce ta faru da ake so a yi maganinta, a cikinku waye yake saduwa da wani a waje?

Wannan mata tai rantsuwa da alkur’ani ta ce, wallahi tun da Allah ya halicce ta bata taba sanin wani da namiji in ba mijinta ba.           Shi kuma ya fadi gaskiya cewa ya sadu da mata sun fi dubu 3, kuma a yanzu ma akwai wasu.

Shi ne likitan ya ce da shi, “To wannan shi ne dalilin da ya sa ciwon ya ki warkewa saboda kuna shan magani kai da matarka, amma sauran masu ciwon da ka sa masu ko ka dauko a jikinsu su ba sa sha, saboda haka kullum ciwon yana nan a jikinka ba zai taba raguwa ba, sai ma karuwa ya ke yi.

Saboda haka wannan matsalar ta ciwon sanyi ta dade tana cutar muyane, gashi har ta kai tana guntule gaban maza, wanda na yi kokari na tuntubi likitocin bature na manyan asibitoci, kamar asibitin Murtala da na Malam Aminu duka a Kano, suka tabbatar min da cewa tabbas akwai mutanen da suka zo gabansu ya guntule, kuma aka yi bincike aka gane cewa ciwon sanyi ne ya haifar da hakan.

Mu ka cigaba akan cewa, to a wannan lokaci da wayar da kai sun yi yawa me yake sanyawa har mutane ciwon sanyi zai yi masu wannan illar ba su nemi magani ba?

Inda muka gane cewa akwai jahilci, akwai kuma kunya, akwai kuma talauci.

Mutum ya kasa gane wurin wa zai je neman magani, in ma asibiti zai nema ya tafi wurin wadanda ba su kware ba, in kuma na gargajiya ne, ya ji wurin wadanda su kawai ‘yan hau ka ci warke ne ba sanin ilmi suka yi ba. Haka kuma in wurin irin mu ne masu yin magani da maganganun da suka zo daga Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam, su ma ka ga mutum ya tafi wurin ‘yan jabu, wadanda su ma suna ji ne don wani na yi ba karanta suka yi da kyau yadda ya kamata ba, wadanda kamata ya yi su dinga sai da maganin ba wai su dinga aikin likitanci ba, ko kuma ko kuma  ba wa mutum maganin ya kasa amfani da shi yadda ya kamata.

Ko kuma a bashi maganin da ya fara amfani da shi in ya ga ciwon ya fara sauki sai ya yar da maganin, saboda haka sai ciwon ya dawo ya fi karfin maganin, gashi nan dai da saurarnsu.

Shi ko jin kunya shi ne, wasu mutane yayin da ciwon sanyi ya kama su, da yake alamunsa na farko da ake gane shi a gaba suke bayyana, sai ya ji kunyar ya tattauna wannan matsalar da wani kamar iyaye ko mata ko miji, ko likita ma, musamman wani yanayi ana cewa ana dauka ta hanyar jima’i ake dauka.

To abinda mutane ya kamata su sani shi ne, in dai ka je wurin mai magani na gaskiya kwararre, to babu yadda za ayi ya tona ma asiri ko da ya sanka, domin mu likitoci muna da alkawari da mu ka yi cewa mun rantse da Allah ba za mu nuna banbanci ga kowa wurin ba da magani ba, haka kuma ba za mu tona masa asiri ba.

Kuma shi ciwon sanyi wasu ba ta saduwa suke samunsa ba, to shi irin wannan ciwon sanyin maganin shi ne:- ‘B/kadani da kash-kash abyadh, Kasaira’ na ci B/ kadan a dinga sha za a warke dardar Akkah Ta’alah. Kuma a dinga cin Karas da lafiyayyen abinci, da kuma man shafawa da yake warkar da ko wace iriyar cutar da ake samunsa a wurinmu.

 

 
Advertisement

labarai