Wannan cigaba ne daga inda aka tsaye dangane da ita wannan cuta ta ciwon sanyin mata ranar Litinin, wato jiya kenan.
Wajen wanke bayan-gida yana daga cikin halayen wasu mata idan sun yi ba haya suna fara wanke duburar su ne daga baya kuma sai gaban su, wasu kuma su na hadawa ne gaba daya, wato gabansu da dubura su wanke su duk a lokaci daya, wannan ba wata dabi’a bace ba mai kyau ga mace, domin kuwa idan kika wanke dubura farko daga baya kuma sai gabanki ko kika wanke su duk a lokaci daya toh zaki iya goga ma farjinki wasu cututtuka dake cikin kashi/bayan gida. Don haka ne ya dai kamata ne a fara wanke farji da farko, bayan kuma an gama wanke shi da ruwa da kyau to sai a wanke dubura.
‘Toilet ko kuma cutar da ake dauka a Masai infection’ wata kalma ce da mutane suka kirkira kuma wadda ta samo asali ne daga mummunar dabi’ar nan ta wanke dubara tare da farji, wanda wasu suke tunanin shi ne ko yin hakan ya ke kawo cutar sanyin-mata. Wani abu kuma sai dai dadilan da suke kawo cutar sanyin mata suna da yawa kamar dai yanda aka yi bayani a can baya, kuma ita kalmar ‘Toilet infection’ ba tada muhalli a cikin ‘Kamus din likitoci a matsayin wai sunan cuta. Mutane ne wadanda ba ma’aikatan kiwon lafiya ba suke amfani da kalmar da nufin ‘vaginal infections’ ko ‘vaginitis’ (kalmar da ma’aikatan lafiya suka fi amfani da ita).
Tsugunno a ban-daki yin tsugunni a bandakin da mutane da yawa ke amfani dashi nada hadari ga lafiya, musamman ban-daki mai dauda da kuma kazanta. Sau da yawa mace zata tsugunna tayi fitsari cikin ban-daki sai fitsarinta ya doki kasa yayi tsalle ya fallatso mata ko kuma ya dawo mata tare da wani ruwan dake kwance a kasa ko fitsarin wata macen.Digo daya na fitsarin mai ciwon sanyi zai iya harbar ki da ciwon idan ya fallatso maki a ga gaba.
Yin amfani da wandon pant na ‘kawar ki, yar’uwar ki ko wata mace wato ku biyu ku rika amfani da shi, kawar ki, kanwar ki ko wata yar’uwarki mutane ne masu iya kamuwa da cuta. Zai iya kasancewa suna da ciwon-sanyi, don haka idan kina jin cewa kin yarda da ita ko kuma kun zama jini da tsoka to ki shirya fama da ciwon sanyi da zai iya harbarki da shi idan kina amfani da wandon su. Koda basu da ciwon, bai kamata ku rinka amfani da pant din junanku ba. Riga kafi dai kowa ya san ai ya fi magani.
Rashin kula wajen yin jima’i saboda kuwa yana da matukar muhimmanci ki kiyaye da jin rauni a farji a lokacin saduwa da maigida. Barin gashin gaba ba’a rage shi ba da kuma yin jima’i tsawon lokaci ko da karfin tsiya na daga cikin dalilan da suke sa mace ta samu rauni a gaban ta. Samun rauni ko fashewar fata cikin al’aura na ba wa su cututtuka kofar shiga jiki su cutar da lafiya da wata cuta ko kuma cututtuka’.
Mataki na biyu da zaki iya dauka shi ne bayan kin san abinda ke damun ki domin a asibiti an bayyana maki, idan har ya tabbata c cutar ta sanyi ce kuma kin sha magani amma baki samu sauki ba, ko kuma kin samu sauki amma baki warke duka ba yana dawowa, toh zaki iya amfani da wannan taimakon da zamu baki :
Ki samu ‘Khal tufah’ [Apple cider vinegar] a Islamic Chemist. Ki tafasa ruwa mai yawa ya yi zafi, idan yayi ‘dumi sai ki samu robar wanka ki juye ruwan ya cika robar, daganan kuma sai ki zuba khal tufah cikin ruwan kimanin yawan kofin shayi (small tea cup) 1 ko 2 cikin robar wankan, sai ki zauna ciki har tsawon minti 15. Bayan kin tashi daga robar sai ki tsane lemar ruwan dake gabanki da tawul mai kyau ya bushe. Sai ki samu man-kwakwa [coconut oil] da auduga ki goge gabanki, man-kwakwa nada sinadarai masu kashe kwayoyin cuta antiviral, antibacterial and antifungal properties] Kiyi amfani da man-kwakwa sau 3 a rana. Za kiyi amfani da Khal tufah kamar yanda mu kayi bayani kullun sau daya a rana har sai kin samu sauki.
Haka nan kuma, zaki iya amfani da Tafarnuwa [Garlic]. Ki samu salar tafarnuwa biyu ko day ki karkare vawon da ledar ta, kiyi matsi dasu da dare idan zaki kwanta bacci sai da safe ki cire ki yar. Tafarnuwa ita ma wani magani ce mai karfi (kuma ‘antibiotic’) , ita ma tana da sinadarai masu kashe cututtuka [antiviral, antibacterial and kuma antifungal properties]. Kuma zaki iya cin tafarnuwa ko amfani da ‘capsules’ nata, idan zaki iya.
Bugu da kari kuma zaki iya neman garin Hulba [Fenugreek powder] a Islamic Chemist da zuma (honey) ki yi shayi, ki yi tasa ruwa ki zuba hulba karamin cokali daya cikin kofin shayi ki motsa, sai ki sha. Kiyi haka safe da dare, har sai kin samu sauki. Idan mace tana da juna-biyu kada tayi haka sai ta nemi shawarar likitan Islamic Chemist/ likitan asibiti da ya san ‘Hulba’ ko kuma wani nmasani amma babu laifi ga mai shayarwa tayi amfani da hulba, hakan zai kara samar mata da ruwan nono. Masu juna-biyu su guji sha-shayen magunguna ba tare da izinin likita ba.
Babu Isassun Wuraren Kiwon Lafiya Matakin Farko A Nijeriya – Minista Ehanire
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa babu isassun wuraren kula da lafiya na matakin farko da za su iya kula da mutanen kasar nan.
Ehinare ya bayyana cewar gwamnati za ta kawo karshen wannan matsalar nan ba da dadewa ba.
Ya ce ana varnatar da kudaden gwamnati ne musamman wadanda aka ware domin gina wurare kamar haka shine babban matsalar da ke kawo tafiyar Hawainiya na shi wannan fanni.
Ya ci gaban da bayanin cewar wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya a kasar nan sun bayyana cewa rashin inganta wuraren kiwon lafiya na matakin farko na daga cikin dalilan da suke kisan mata a kalla kashi 80 cikin 100 a Nijeriya.
Tolu Fakeye ya sanar da hakan ne a taron kungiyar likitocin da suka kware a kimiyyar hana yaduwar cututtuka na kasa (EPiSON) da ake yi a garin Jos, jihar Filato.
EPiPSON tare da hadin guiwar PACFaH@Scale sune suka shirya wannan taro domin tattauna irin gudunmawar da ita kungiyar za ta iya yi a wajen tsara hanyoyin da za su ci gaba da hana yaduwar cututtuka a Nijeriya da magance su.
Da yake jawabinsa Fakeye ya ce rashin samun shugabanni na gari da kuma wawushe kudaden da ake ware wa su cibiyoyin kiwon lafiya na daga cikin matsalolin da suke kawo cikas wajen harkar samar da kiwon lafiya a cibiyoyin tun bayan da aka kafa su.
Ya kuma ce sauran matsalolin da ya mamaye cibiyoyin kiwon lafiya sun hada da rashin kwararrun ma’aikata, rashin ingantaccen wuraren aiki, rashin kayan aiki da sauran su.
Idan ba a manta ba shekaru hudu da suka wuce gwamnatin Buhari ta bayyana cewa za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 10,000 a kasarnan.