Sister Iyami Jalo Turaki" />

Ciwon ‘Ya Mace… Rashin Ilimin ‘Ya Mace…

Sister Iyami Jalo Turaki 08064666847

sisteriyami@gmail.com

 

Wannan karon hangen nawa ya koma bangaren ilmi ne wanda na hango irin matsalolin da rashin ilimin ‘ya mace ke haifarwa a cikin al’umma. Tabbas rashin ilmi ga ‘ya mace kalubale ne kuma babbar illa ce ga rayuwarta baki daya. Ilmi na da matukar muhimmanci musamman ga mata saboda su ne iyayen al’umma. Mace sai ta na da ilmi za ta samu sauki wurin tafiyar da rayuwarta, ilmi haske ne wanda zai haskawa mace yadda za ta tafiyar da al’amurar rayuwar ta cikin sauki.

 

Idan mace ba ta da ilmi dole ta samu nakasu a cikin rayuwarta, ilmi ginshiki ne kuma gishiri ne na zaman duniya, kuma hanya ce ta samun lahira. Mata da yawa kan dauka cewar sun yi girma ko sun wuce fita neman ilmi daga lokacin da su ka fara tara yara shikenan, Wanda a daidai wannan lokaci ya dace ta nemi ilmi don ta samu sauki wurin inganta tarbiyyar yaranta. Sai da ilmi za ki samu hanyoyi da dabarun zama da maigida. A wannan zamani komai sai da ilmi ke samuwa, yawaitar mata marassa ilmi kamar koma baya ne ga wannan al’umma, domin sai mace na da ilmi za ta yi bautar ubangiji, sai da ilmi za ta san hanyoyin kula da maigida, sai ta na da ilmi za ta san muhimmancinta ga yaranta, sanin muhimmancin ilmi da yin aiki da shi shi ne cigaban kowacce al’umma. Sai da ilmi rayuwar mace a duniya za ta inganta, sai da ilmi mace za ta gyara lahirarta.

 

Matsalolin Da Rashin Ilmin ‘Ya Mace Ke Haifarwa:

Rashin ilmin ‘ya mace na da matsaloli masu tarin yawa, kadan daga cikin su su ne :

1:Rashin ilmi kan haifar da tabarbarewar tarbiyya.

2:Rashin ilmi kan haddasa mummunar gaba.

3:Rashin ilmi na sa mutum tunani marar ma’ana..

4:Rashin ilmi na haddasa yawan fadace-fadace.

5:Rashin ilmi na haifar da mummunar kishi a zuciyar mai ita.

6:Rashin ilmi na haddasa zargi.

7:Rashin ilmi na raba mace da imaninta.

8:Rashin ilmi kan haifarwa mace matsala a gaba daya rayuwarta.

Da sauransu

 

 Ina Mafita?

Mafita anan ita ce :

1.Mu nemi ilmi a duk in da mu ka tsinci kanmu cikin birni ko kauye.

2: ka da mu yarda tarin yara ko yawan shekaru su zama sila na hana mu neman ilmi.

3:idan mun samu ilmi mu yi kokari wurin ganin mun yi aiki da ilmin.

4:sai da ilmi za mu gyara mu”amalar mu da kowa.

5 :Mu tashi wurin ganin mun kai ga nasarar samar da ilmin da zai amfanar da al ‘ummar da muka samu kanmu a ciki.

 

Shawara Ga ‘Yan Uwa Mata…

Hakika ilmin ‘ya mace abu ne me matukar muhimmanci, kar mu sake a barmu a baya ta bangaren neman ilmi, duk al’ummar da ta ke da karancin mata masu ilmi wannan al’umma za ta zamanto koma baya .samun ilmin mace daya tamkar samar da ilmi ne ga al’umma baki daya.

Exit mobile version