Ciyamomi 8 Na Jam’iyyar APC Sun Koma PDP A Zamfara

Shugabannin kananan hukumomi 8 sun sauya sheka, daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar. Sunayen ciyamomin da suka sauya shekar sun hada da: Alhaji Muhammadu Umar, shugaban karamar hukumar Birnin Magaji; Alhajj Salisu Isah Dangulbi, shugaban karamar hukumar Maru; Alhaji Nasiru Zarumi Masamar mudi, shugaban karamar hukumar Bukkuyum; Alhaji Ahmed Balarabe Anka, shugaban karamar hukumar Anka.

Alhaji Balarabe Anka ne ya sanar da manema labarai bayan taron da suka yi gwamnan. Ya ce sun yanke shawarar komawa PDP din ne sakamakon salon shugabancin Gwamna Matawalle da kuma yadda ya dawo da zaman lafiya a jihar cikin kankanin lokaci.

Alhaji Anka ya jaddada cewa, an samu daidaituwar siyasa, hadin kai da zaman lafiya a yayin da ya cika kwanaki 100. Hakan yana nufin kwarewar Matawalle shugabanci.

Shugabannin kananan hukumomin sun koma PDP din ne tare da magoya bayansu.

A yayin karbar shugabannin kananan hukumomin, Gwamna Matawalle ya mika godiya ga shugabannin tare da jinjina musu na hangen nesan da suka yi na komawa PDP a Zamfara.

Gwamna Matawalle yayi alkawarin mutunta su tare da tafiya tare da wadanda suka sauya sheka.

Exit mobile version