Ciyarwa Na Kara Bunkasa Ilimi A Gezawa

Shugaban hukumar kyautata cigaban rayuwar al’umma na karamar Hukumar Gezawa, Malam Isma’il Usman Jogana ya bayyana ciyarwa da Gwamnatin Jahar Kano keyi a makarantu a yankin da cewa sun gode wa Allah bisa fito da tsarin ciyarwar ga yan aji hudu,biyar da shida da hakan ke bunkasa harkar ilimi sosai a Gezawa.

Ya yi nuni da cewa yanzu yara da basa zuwa makaranta a baya yanzu sun koma, tsarin daukar yara ya karu sosai ya nunka, abinda ake dashi a baya hakan na da nasaba da yanda nasarar ciyarwar ya kawo, duba da a baya akwai matsaloli na matsin tattalin arziki da hakan kesa iyaye su tura yara talla amma sakamakon wannan abinci da ake bayarwa ya jawo hankalinsu wasu kuma da kansu ma yaran suke kai kansu makarantun domin su amfana,hakan yasa iyayen yara sun samu sassauci da sauki dan haka yara ma basa danuwa sai an basu kudin tara.

Malam Isma’il Usman Jogana ya ce, a baya dama akwai tsarin ciyarwa na Gwamnatin tarayya da ake ga yan aji daya da biyu da Uku wannan tasa a dukkan makarantu ba wani aji da aka bari a kasa ba’a ciyar dashi daga yan aji daya zuwa shida, akwai wadataccen abinci da yara ke samu wannan yasa makarantu ke cikar kwari.

Yace mata da suke aikin dafa abincin na makarantu suna abinda yakamata wajen inganci da dandano da tsafta kamar yanda aka tsara a samar dashi mai kayan gina jiki,a ranar Litinin dafa shinkafa da wake da ake ana amfani da kayan gina jiki.A ranar Talata anayin dambu na tsakin masara da ake sawa gyada da sauran kayan gina jiki.A ranar Laraba ayi dafadukan makaroni sannan ranar Alhamis ayi Alala,ran juma’a ana raba musu buskit.Duk tsarin ciyarwar na Gwamnatin jaha data tarayya dayane.

Shugaban na “CPC” Na Gezawan yace sunada makarantu guda 135 dake tsarin ciyarwar Gwamnatin tarayya.A tsarin ciyarwar Gwamnatin jahar Kano kuma akwai makarantu 78 a tsarin ciyarwar. Gwamnatin tarayya tana ciyarda yara 23,940 a Gwamnatin jaha kuma akwai dalibai 19,654 idan aka hadasu duka akwai dalibai samada 40,000 da ake ciyarwa a kowace rana daga Litinin zuwa Juma’a.

Yace a tsarin bada ilimi kyauta da Gwamnatin Kano take,sun bada kayan makaranta kyauta ga dalibai 25,000 kuma akwai mutane da dama da suke taimakawa bada ilimi kyauta ta bada tallafin kayan makaranta da littattafai a makarantu.

Ya yabawa irin hadin kai da gpyon baya da sashen ilimi na karamar hukumar Gezawa karkashin sakataren ilimi Alhaji Abdullahi Ajuji da dukkan masu ruwa da tsaki da malaman makarantu ke basu dan ciyarda ilimi gaba

Exit mobile version