Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Nazifi Yahaya zai je gwaji kungiyar Club Brugge ta kasar Belgium.
Wani kusa a kungiyar kwallon kafan ta Pillars ya bayyanawa manema labarai cewa tabbas ya san cewa dan wasan ya je Abuja domin neman tafiya a hukumar kula da shige da fice ta kasa, amma har yanzu ba shi da masaniya akan yaushe za a yi tafiyar.
Nazifi ya wakilci Nijeriya a gasar ‘yan kasa da shekaru 15, ya kuma zura kwallaye a wasan ‘yan kasa da shekaru 17 da aka buga a kasar Afirika Ta Kudu.
An dai taba alakanta dan wasan da komawa Atletico Madrid ta kasar Spaniya.