Bello Wang Na CRI" />

CMG Na Shirya Bikin Kade-kade Da Raye-raye Na Murnar Shiga Sabuwar Shekara

A yayin da ake jiran ganin bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara da za a gabatar da shi a ranar 4 ga watan Fabrairu, wato jajibirin bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, kan telabijin, a yau Alhamis, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya kira taron manema labaru, don yin bayani kan fasahohin al’adun da za a nuna, gami da sabbin fasahohi na zamani da za a yi amfani da su wajen bikin.
Jiang Wenbo, wani jami’in kamfanin CMG ya bayyana cewa, za a yi amfani da fasahohi mafi ci gaba, da na’urori mafi inganci wajen tsara bikin na murnar sabuwar shekara. Sa’an nan fasahohin da za a yi amfani da su wajen nuna bikin sun hada da 4K, 5G, BR, AR, da AI, da dai makamantansu. (Bello Wang).

Exit mobile version