A ranar 27 ga wata ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kaddamar da gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya a birnin Beijing.
Babban daraktan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, masana’antar mutum-mutumin inji ta zama wata muhimmiyar alama ta auna matsayin wata kasa ta fuskar kimiyya da fasahar kere-kere da kuma masana’antar kere-kere na babban mataki. Kasar Sin ta zama kasa mafi grima a duniya wajen kera mutum-mutumin inji da yin amfani da su. Ta hanyar dogaro da babban dandalin watsa labaru mai karfi, gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya ta CMG za ta nuna nasarorin da aka samu wajen kera mutum-mutumin inji ta kowane bangare, ta yadda za a hada karfin kimiyya da fasaha da kuma al’adun gargajiya waje guda, ta yadda ainihin kirkire-kirkire da ayyaukan kula da dan Adam za su kyautata tare. Ana sa ran wannan gasa za ta sa kaimi ga ci gaban fasahar mutum-mutumin inji da kuma ba da gudummawa wajen gina kasar Sin mai karfin kimiyya da fasaha da gina al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama. (Mohammed Yahaya)