CRI Hausa" />

CMG Ya Kaddamar Da Gwajin Fasahar 8K A Tashar Talabijin

A yau Litinin 1 fa watan Fabarairu, babban gidan radiyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya kaddamar da gwajin fasahar 8K a kafar talabijin, domin samar da managartan hotunan talabijin masu matukar kyawun gani.

Da yake tsokaci game da hakan yayin bikin kaddamarwar, babban daraktan CMG Shen Haixiong, ya ce gwajin watsa shirye-shirye ta wannan fasaha mai inganci, da hadin gwiwar manyan kamfanonin sadarwa na wayar salula, ya zama irin sa na farko a duniya.
Ya ce a karon farko, Sin na gwajin fasahar talabijin ta 8K Ultra HD kai tsaye, da kuma fasahar watsa shirye shiryen talabijin na 8K ta amfani da fasahar 5G. Jami’in ya kara da cewa, nasarar gwajin fasahar 8K Ultra HD a kan tashar talabijin, ta tabbatar da nasarar da aka cimma a fagen amfani da fasahar “Ultra HD” a Sin.
A jajiberin bikin sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar Sinawa, wato ranar 11 ga watan Fabarairun nan, CMG za ta kuma watsa shirye shirye kai tsaye kan tashar CCTV, inda za a kalli bukukuwan da aka tsara ta amfani da fasahar 8K Ultra HD. Shirin zai kasance irinsa na farko a duniya, da za a watsa ta amfani da fasahar 8K UHD, mai fitar da mafi nagartar hotuna. (Saminu Hassan)

Exit mobile version