CRI Hausa" />

CMG Ya Nuna Wani Shiri Dake Kara Bayyana Al’Adun Sinawa

A yau da yamma, jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya nuna wani shirin murnar bikin baraza na bana, ta hanyar amfani da fasahohi na zamani, domin kara bayyana al’adun Sinawa ga masu kallo da sauraro dake sassa daban-daban na duniya.

Bikin nune-nunen, wani gagarumar liyafa ce da CMG ya shirya, a jajibirin bikin baraza. Shirin ya kunshi fasahohi da suka hada da wake-wake da raye-raye, da wasan kwaikwayon gargajiyar kasar Sin. A cikin sama da shekaru 30 da suka gabata, wannan ya kasance al’ada a ko wace sabuwar shekarar gargajiyar kasar, inda iyalai ke haduwa a jajibirin sabuwar shekara, don kallon nune-nunen bikin da ake shiryawa.
A nune-nunen na bana, an nuna nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin kawar da talauci, da kandagarki da hana yaduwar annobar COVID-19, da ma nau’o’in al’adun gargajiya. Baya ga shirye-shiryen da aka saba watsawa ta talabijin, akwai kuma sabbin kafofin sadarwa da dama na zamani, kamar “kwaikwayon tunanin dan-Adam da 3D” wadanda ke nishadantar da jama’a. Haka kuma, akwai kafofin watsa labarai sama da 600 daga kasashe da yankuna sama da 170, ciki har da Amurka da Faransa da Italiya da Rasha da Brazil da Australia da Indiya da hadaddiyar daular Larabawa da Malaysia da Afirka ta kudu, wadanda suka watsa nune-nunen liyafar bikin bazara na bana kai tsaye.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version