Jiya Talata, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya shirya bikin karanta wasu muhimman bayanai domin murnar cika shekaru 80 da fara gudanar da harkokin rediyo na al’ummar kasar Sin a Beijing.
Masu gabatar da shirye-shiryen rediyo sama da 40 daga CMG sun karanta wasu muhimman bayanan da aka rubuta, wadanda suka taka muhimmiyar rawa a tarihin kasar Sin, domin shaida irin gwagwarmayar da aka yi domin bunkasa harkokin rediyo na al’umma cikin shekaru 80 da suka gabata.
A ranar 30 ga watan Disambar shekara ta 1940, gidan rediyo mai suna Xinhua dake birnin Yan’an, ya fara watsa shirye-shirye, abun da ya nuna fara soma harkokin rediyo na jama’a na kasar Sin. A watan Maris din shekara ta 2018 kuma, an kafa babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, al’amarin da ya bude sabon babi a harkokin rediyo na jama’a.
A halin yanzu CMG yana da kafofi guda 23 dake watsa shirye-shiryensa ga masu sauraro dake cikin babban yankin kasar, gami da yankunan Hong Kong da Macau da Taiwan da kuma sassan kananan kabilu, yana kuma amfani da wasu harsuna 44 wajen watsa shirye-shiryen rediyo ga ketare. Ya zuwa shekara ta 2019, yawan masu sauraron CMG a duk fadin kasar Sin ya zarce miliyan 600. (Mai Fassara: Murtala Zhang)