A ranar 21 ga watan Agusta ne aka gudanar da bikin cudanyar al’adu mai taken “Sautin zaman lafiya”, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG da ofishin jakadancin Sin dake hadaddiyar daular Larabawa suka karbi bakunci, a Abu Dhabi dake hadaddiyar daular Larabawa.
Kazalika, duk dai a ranar, an yi bikin cudanyar al’adu mai taken “Sautin zaman lafiya” wanda CMG da cibiyar al’adun kasar Sin dake birnin Seoul, da dakin tunawa da gwamnatin wucin gadi na kasar Koriya ta Kudu suka shirya a birnin Seoul dake kasar ta Koriya ta Kudu. Shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a yayin bukukuwan guda biyu.(Safiyah Ma)