Khalid Idris Doya" />

CNI Ta Karrama Shugaban ‘Correspondents Chapel’ Na Bauchi Da Lambar Yabo

Wata kungiyar da ke fafutakar inganta zamantakewar aure mai suna ‘Couple Network International’ ta karrama shugaban wakilan kafafen sadarwar na jihar Bauchi, Mista Segun Awofadeji, da lambar yabo ta jinjina a bisa gudunmawar da yake bayarwa kan harkar yada labarai musamman ga kungiyar da al’umma gaba daya.

Kungiyar, ta karrama shine a wajen wani taron liyafar cin abinci da bikin shakatawa da ta shirya wa ma’aurata, an yi taron ne da zimmar tunatar da ma’aurata hanyoyin inganta zamantakewar da ke tsakaninsu, taron wanda ya gudana a cikin kwalejin kimiyayya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya da ke Bauchi.

Da ya ke jawabinsa a wajen taron, shugaban kungiyar sulhunta ma’autara ta ‘Couples Network International’, Rabaran Okafor T. Emefesi ya shaida cewar kungiyar za ta kaddamar da cibiyar shakatawa da kyautata rayuwar ma’aurata a fadin duniyar nan domin aure yake samun kargo a kowani lokaci.

Wakazalika, Rabaran Okafor Emefesi ya daura da cewar za a samar da gidan talabishin ta yanar gizo wacce za a kebenceta kawai domin sabuntawa da kyautata zamantakewar iyali.

Shugaban ya ce an kafa kungiyar ne da zimmar gina ginshikin da zai kai ga daurewar aure a tsakanin mabiya addinin Kirista da kuma baiwa aure muhimmanci a tsakanin ma’aurata kana da kareshi daga rushewa ko rugujewa.

Sauran ababen da kungiyar ta sanya a gaba har da kokarin kyautata kiwon lafiya a tsakanin ma’aurata da iyalansu, da kuma tabbatar da yin addu’o’i na musamman domin kariyan kai ga dukkanin matsalolin da ma’aurata ke fuskanta domin kare rayuwar aure daga fadawa cikin garari.

Ya ce, kawo yanzu sun cimma nasarori masu tarin yawa, wadanda a ciki da wajen Nijeriya za su tabbatar da cimma muradinsu na kyautata zamantakewar aure a tsakanin ma’aurata.

Rabaran din ya shaida cewar ba abun burgewa ba ne yawaitar samun matsalolin aure a tsakanin jama’a, yana mai nuna gayar takaicinsa a bisa yadda wasu ke daukar hanyar rabuwar aure a maimakon sulhunta lamarin ko kuma gyara matsaloli idan an samu sabani a tsakani.   

Kungiyar dai ta yi amfani da wannan damar wajen karrama wasu fitattun ‘yan jarida da suka baiwa kungiyar agaji ta fuskacin yada shirye-shiryenta a cikin al’umma, shugaban wakilan kafafen sadarwar (Correspondents Chapel reshen jihar Bauchi), Kwamared Segun Awofodeji da tsohon Daraktan da ke kula da gidajen rediyon al’umma na kafar sadarwar BRC, Mista Joseph Ecko Otokpa, gami kuma da jami’in hulda da jama’a na jami’ar ATBU Andiy Eheme suna daga cikin wadanda suka amshi lambar yabo a wurin taron.

Da ya ke jawabin godiya ga uwar kungiyar a madadin wadanda suka amshi lambar yabon, Kwamared Segun Awofadeji ya nuna gayar godiyarsa ga kungiyar a bisa zaboshi da bashi wannan lambar ta yabo, yana mai shan alwashin ci gaba da zage damtse don yi wa jama’a aiki tukuru.

Awofadeji ya daura da cewar bayar da gudunmawa domin kyautata zamantakewar aure abu ne da ke da gayar muhimmanci a cikin al’umma duba da yadda wasu ke sake da lamarin aure a wannan zamanin.

Daga cikin abubuwan da su ka wakana a wajen taron sun hada da addu’o’i na musamman a bisa bin tsarin koyarwar addinin Kirista, wakokin yabo da karfafa ma’aurata, kasaitaccen walimar ci da sha da kuma shakatawa a tsakanin ma’aurata inda kowani magidanci ya hallara da matarsa a wajen taron.

Exit mobile version