Abba Ibrahim Wada" />

COVID-19: Za A Hukunta Dan Wasan Manchester City Walker

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta  Manchester City, Kyle Walker zai fuskanci hukunci, bayan da ya karya dokar hana fita inda ya shirya wani bikin da ya gayyato karuwai a unguwar da yake zaune.

Walker ya nemi afuwa ya kuma yi kira da kowa ya zauna a gida a lokacin da ake daukar matakan hana yada coronabirus sai dai a wani bayani da Manchester City ta fitar ta ce dabi’ar da dan wasan tawagar Ingilan ya nuna ta ci karo da halayyar da ya kamata ya gwada a matsayinsa na abin koyi ga na baya.

Ta kuma kara da cewar za ta gudanar da bincike kan dan wasan domin fayyace abinda ya faru a lokacin da aka bukaci kowa ya killace kansa sakamakon annobar cutar Corinabirus wadda ta addabi duniya a halin yanzu.

Gwamnati ce ta bukaci mutane su bayar da tazara a lokacin yin mu’amala su kuma zauna a gida a kokarin dakile yada coronabirus kuma tuni aka hana fita daga gidaje a yankin burtaniya gaba daya da ragowar wasu daga cikin kasashen turai.

Amma daga baya dan wasan ya bayar da hakuri inda ya bayyana cewa yayi kuskure kuma yana neman afuwa daga wajen shugabannin kungiyar da jami’an tsaron garin na Manchester da kuma gwamnatin burtaniya gaba daya.

Tun a watan daya gabata ne aka dakatar da wasannin firimiya gaba daya sakamakon yaduwar cutar sanann itama gasar kofin zakarun turai ta Champions League an dakatar da ita har sai baba ta gani.

Exit mobile version