Connect with us

Ka San Jikinka

Corona A Jikin Xan Adam

Published

on

Corona A Jikin Dan Adam

 

‘Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke zakulo muku bayanai game da jikin  dan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki.

Kimanin sati hudu kenan ina bayani akan yadda fatar dan adam take, da muhimmancinta a jikinmu. Yau da Yardar Sarkin halitta, zan dauki sabon maudu’i mai muhimmancin gaske domin yin rubutu a kai.

Duba da yanayin da muka tsinci kanmu a ciki na annobar wannan cuta mai suna “Corona virus”, inaga ya dace nayi rubutu domin karawa ‘yan uwa bayanin yadda cutar ta ke da irin ta’annatin da takeyi a jikin dan adam.

 

Bari mu fara da sanin Mece ce ainihin ita “corona virus”?
Wannan wata kwayar cuta ce mai sanya sarkewar numfashi da kuma dakile musayar iska tsakanin huhun dan adam da kuma duniyar da yake ciki.

To Yaya siffar “Corona virus” take?

kwayar cutar mulmulalliyya ce, kuma kewaye take da wani vawo mai maiko irin na mai. Shi yasa ake so mu yawaita wanke hannayenmu da sabulu, saboda kunsan shi sabulu yana wanke maiko. A jikin vawon da ya kewaye ta, akwai wasu halittu masu tsini da ke ko ina a jikinta; wato kamar dai yadda bushiya take da kaya ko ina a jikinta, haka ma Corona virus take.

Ta ina cutar take shiga jikin dan adam?

Wannan cuta tana shiga jikin dan adam ne ta wadannan kafofi: hanci, baki, da kuma ido.

Ta Yaya ake daukar wannan cuta?

Babbar hanyar da ake daukar wannan cuta itace ta mu’amala da wanda ke dauke da cutar, ko tava wani abu da ya tava ko ta tava. Shi yasa malaman lafiya suke ta jaddada mana cewa mu dinga yawan wanke hannayenmu da sabulu.
Hannun dan adam matattara ce ta taruwar kwayoyin cuta masu dumbin yawa; wasu masanan sunyi kiyasin cewa hannu zai iya tattare kwayoyin cutuka sama da dari a rana. Saboda tun lokacin da Garin Allah ya waye, ka tava wancan, ka gaisa da wancan ka goge wancan, da sauransu. Ta haka muke cika hannayenmu da kwayoyin cuta ba tare da mun sani ba.

Ta Yaya cutar take yaduwa?

Cutar tana yaduwa ne ta hanyar vurvushinta da mai cutar ya yiyo atishawar su, daga nan sai su bi iska a inda idan aka samu akasi akwai wani mutumin a kusa da wanda yayi atishawar, to sai ya shaki kwayoyin ta hanyar numfashi.

Ina ne matattarar wannan cuta?

Da zarar wannan kwayar cutar ta sauka a a jikin dan adam, babban inda ta ke hari shi ne kwayoyin halittar da ke shimfide a makogwaronka, huhu, da sauran hanyoyin iska. Da zarar wannan cuta ta samu zuwa wadannan wurare, to sai ta samu wani sashe wanda zata makale. Kar ku manta tana da ‘kaho’ da yawa a jikinta.

Wane irin ta’adi wannan kwayar cuta ta ke yi?

Babbar varnar da zata fara yi ita ce mayar da halittun makogwaro ko kuma halittun koma wane sashe na jiki ne inda ta sauka ya zama cibiyar samar da sabbin kwayoyin cutar Corona virus.

Daga kwana daya zuwa biyar har zuwa sati guda da cutar tayi a jikin dan adam, babu wasu alamu da ke bayyana cewa mutum ya kamu, amma tana ciki tana ta tsara yadda zata yaki sauran kwayoyin halittar jiki.

Yaya alamomin kamuwa da wannan cuta su ke?

Bayan wadannan kwanaki, sai dan adam ya fara jin alamu na ciwon kai, makaki ko dadewar makogwaro, zazzavi, numfashi sama-sama, da kuma ciwon kai.

Ta yaya kwayar cutar take kara yawa a jikin dan adam?

Wannan cuta ta Corona virus tana da wasu abubuwa kamar kugiya ko kaho da ta take amfani da su wajen makalewa a kwayoyin halittun jiki. Yayin da wannan cuta ta kama wani sashe a jiki, to zata umarni kwayoyin halittar jiki na wannan waje da su dakatar da komai na gudanarwar jiki, kuma su fara hayayyafar kwayoyin cutar corona ka’in da na’in.

A madadin kwayar halittar jiki ta samar da kwafin sabuwar kwayar halittar jiki, sai ta samar da kwafin sabuwar halittar Corona virus; ita ma kuma sabuwar da aka haifa, zata haifi wata sabuwar kwayar cutar, haka abin zai ta tafiya har Corona virus ta kafa sansani a inda ta sauka, idan ta hanci ta shiga, har sai ta mamaye mafi yawan hanyoyin iska: bututun numfashi da huhu.

Wani likita wanda ya kware a nazarin cututuka masu yaduwa yace: “idan wannan kwayar cuta ta shiga huhun dan adam, musamman ‘kokon’ musayar iska da ake kira “alveoli”, ta kan sa ya taasa ko ya kumbura, a sanadiyyar haka iskar oksijin ba zata iya ketawa daga kokon musayar iskar ba izuwa jijiyar jini, wadda ita jijiyar ce za ta dauki jinin ( idan an zuba masa iskar) ta kaiwa zuciya, ita kuma zuciya ta rabawa sassan jiki. To haka ne ke sai mutum ya kasa numfasawa yadda ya kamata”.

Mene ne illar faruwar hakan?

Wannan taasawa da ake samu a inda ake musayar iska kan sa ruwa ko mugunya da mattatun kwayoyin halittun jiki wadanda Corona ta lalata su taru a wajen, to kunga hakan zai kawo nakasu ga samun lafiyayyen numfashi kenan. Idan aka samu akasi wannan ruwa yayi yawa a inda ake musayar iska na sassa daban daban a cikin huhu, babu wani tallafin numfashi da zai amfani mara lafiyar a wannan lokaci, daga nan kuma zai ce “ga garinku nan”.

 

Banda huhu da hanyoyin iska, shin cutar Corona virus tana kama wasu wuraren a jikin dan adam?

Amsar ita ce “E”. Tana kama kayan ciki, abinda ya kama tun daga jannai (wato bututun abinci) har zuwa dubura. Shi yasa wasu wadanda suka kamu da cutar ke tsuga gudawa ko kuma su dinga fama da rashin narkewar abinci. “Bugu da kari, wannan muguwar cuta kan kama koda, hanta ko zuciya. Kuma idan akayi rashin sa a ta sauka a wadannan gurare, ta kan lahanta su sosai” inji Dr. Schaffner, kwararren likita a fannin cutuka masu yaduwa.

Abin tambayar anan shi ne, me yasa cutar take wa wasu mutanen kamun kazar kuku, wasu kuma take cinsu a hankali? Akwai dalilai; Amma binciken lafiya ya nuna cewa hakan yana da alaka ne da karfin garkuwar jikin dan adam a lokacin da cutar ta shiga jikinta ko jikinsa.

Mutane wadanda suka dade da cutuka a jikinsu sannan kuma suka kamu da wannan cuta, abin bai fiye zuwa musu da sauki ba. Su ma tsofaffi haka, duba da cewa garkuwar jikinsu tayi rauni saboda shekaru. Sauran mutane wadanda da ke da ragowar jini a jika, abin kan zo musu da sauki.

Yaya batun matakan kare kai daga kamuwa da wannan cuta?

  • A dinga bin shawarar malaman lafiya.

*A dinga wanke hannu akai akai domin kawar da cutar daga hannu, da kuma rage yaduwarta

*A guji musabiha, shafar fuska, idanu

*A bar tazara tsakaninku da sauran mutane, a rage yawan cudanya.

*A dukufa sosai wajen yin addu’o’ i dan neman sauki daga Allah.

Allah ya maganta ma na wannan annoba, Ameen.

Mu hadu a mako na gaba idan Allah ya kai mu.
Advertisement

labarai