Bello Hamza" />

Coronavirus: Harkokin Kasuwanci Za Su Cigaba A Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya–NPA

Hukumar tashoshin jiragen Ruwan Nijeriya ta bayyana cewa, ba ta da
shirin kulle tashoshin jiragen ruwan Nijeriya duk kuwa da barkewar
yaduwa cutar coronavirus da ake fama da shi a fadin tarayyar kasar
nan.
Hukumar ta bayar da wannan sanarwa ne ta hannun babban jami’in watsa
labaranta, Mista Adams Jatto, ya kuma ce, sun dauki wannan matakin ne
a mastayin bin umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Daga nan ya kuma kara da cewa, a halin yanzu an kammala dukkan
shirye-shirye na ganin dukkan harkokin kasuwanci da hada-hadar da ake
yi a tashoshin jiragen ruwan Nijeriya na tafiya ba tare da wani
matsala ba.
Ya ce, cikin matakan shi ne matakan kariya daga cuta da kuma bayar
cikakken tsaro ga masu ruwa da tsaki da ma’iakatan hukumar don su
gudanar da harkokinsu ba tare da wani matsala ba, a kan haka ya
shawarci dukkan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da bin dukkan
dokokin da aka sanya a tashoshin jiragen ruwan don ganin komai yana
tafiya yadda yakamata.
Sanarwa ta kuma ci gaba da bayyana cewa, “Ana umartar ta dukkna
kamfanoni da masu ruwa da tsaki a harkokin tafiyar da tashar jiragen
ruwan Nijeriya su tabbatar da sun bayyana a wuraren gudanar da
ayyukansu kamar yadda Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya umarta na
cewa, a cigaba da harkoki a tahsar jiragen ruwan Nijeriya, musamman na
Legas.
“Hukumar tashare jiragen ruwan na tabbatar wa dukkan masu ruwa da
tsaki da cewa, za ta tabbatar da samar da dukkan abubuwn da ake bukata
don ganin ana gudanar da harkokin kasuwanci yadda yakamata ba tare da
wani matsala ba”
Manema labarai da suka ziyarci tashar jirgin ruwan Apapa dake Legas,
sun lura da cewa, lallai harkokin kasuwanci ya ci gaba yadda ya kamata
sai dai matsalar rashin budewa bankuna wanda hakan ya kawo cikas a
wasu bangarori na hadahahar da ake yi a tashar.
Duk da cewa, ana iya biyan wasu kudade ta intanet amma akwai kudaden
wasu abubuwan da ba za a iya biya ta intabet ba, musamman abin day a
shafi kudin kwastam.
Ana dai cigaba da yaba wa shugabar hukumar, Hajiya Hadiza Bala Usman
akan yadda ta jajirce na gani an bi umarnin Shugaban kasa Muhammadu
Buhari na dawo a ci gaba da harkoki a tashar jiragen ruwan duk kuwa da
halin da ake ciki.
Exit mobile version