Bello Hamza" />

Coronavirus: Shugabar Kungiyar NAWOJ Ta Yi Gargadi Kan Nuna Bambanci Ga Wadanda Suka Warke

A ranar Juma’a ne shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa ‘Nigerian Association of Women Journalists (NAWOJ)’ reshen jihar Legas ta shawarci ‘yan Nijeriya kan su daina nuna banbanci ga wadanda suka warke daga cutar COVID-19.

Shugabar kungiyar, Misis Adeola Ekine, ta bayyana haka ne a takardar sanarwa da ta raba wa manema labarai a garin Legas. Ekine ta kuma kara da cewa, ya kamata ‘yan Nijeriya su nuna wa wadanda suka warke cikakken soyaya su kuma guji nuna musu kyama da wariya. “Ya kamata a nuna musu soyaya tare da rungumarsu musammnan ganin halin da suka shiga sakamamon zaman da suka yi a cibiyoyin kebe jama’a tare da kuma irin magungun da suka karba a yayin da suka fuskanci cutar,” inji ta.

Shugabar kungiyar ta kuma ce, ya kamata a fahinci cewa, cutar Coronabirus ba wai tana nufin mutum ya kama hanyar zuwa lahira bane. Daga nan ta kuma yaba wa gwmnatin jihar Legas da kuma dukkan ma’aikatan lafiya a bisa kokarin da suke yi na ganin an samu saukin cutar a jihar Legas.

Ta kuma bukaci ‘yan jarida su kara kaimi wajen gunadar da ayyukansu musamman ganin akwai bukatar a fadarkar da al’umma hanyoyin kariya daga cutar, ta kuma bukaci a hada da yara kananan wajen fadakarwar don suma cutar bata bar su a baya ba.

Exit mobile version