Abba Ibrahim Wada" />

Coronavirus Ta Kashe Tsohon Shugaban Kungiyar Marseille

Tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar Olympic Marseille da ke Faransa kuma dan asalin kasar Senegal, Papa Diouf ya rasu bayan kamuwa da cutar coronabirus wadda ta kamashi a watan daya gabata.

 

Diouf ya mutu yana da shekaru 68 bayan kamuwa da cutar coroanabirus kamar yadda danginsa suka sanar sai dai tuni shugabannin kungiyoyi da tsofaffin ‘yan wasan da yayi aiki dasu suka fara nuna alhininsu.

 

Marigayin wanda aka haifa a kasar Chadi,yana da takardar shaidar zama dan kasa a Faransa da kuma Senegal kuma a farkon shekarunsa ya buga kwallon kafa a kungiyoyi da dama musamman a Faransa.

 

An kwantar da shi ne a asibitin birnin Dakar dake kasar Senegal  bayan ya kamu da coronabirus, ya yin da ya zama mutun na farko da cutar ta aika lahira a Senegal duk da yawan masu kamuwa da ita a kasar.

 

Diouf ya jagoranci kungiyar Marseille tsakanin shekarar 2005 zuwa 2009, sannan ya taimaka wajen gina kungiyar har ta lashe kofin gasar Lig 1 a shekarar 2010 har ila yau ya taikamawa kungiyar wajen rainon matasan ‘yan wasa.

 

Tsohon dan wasan tawagar Faransa da Liberpool, Djibril Cisse ya buga wa Marseille kwallo a lokacin da Diouf ke shugabanci inda ya ce kwallon kafa ya yi asarar babban jami’i, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter ya kara da cewar lokaci ne na bakin ciki da rashin Diouf.

Exit mobile version