Nasir S Gwangwazo" />

Coronavirus Ta Sake Kutso Wa Nijeriya

Fitacciyar annobar cutar nan ta COVID-19, wato wacce a ka fi sani da suna Coronabirus, ta sake kunno kai cikin Tarayyar Nijeriya, inda ta kutso ta hannun wata mace, wacce ta sauka a birnin Ikko daga birnin Landon.

Gwamnatin Jihar Legas ce ta tabbatar da haka a jiya Talata ta bakin Kwamishinan Lafiya na jihar, Akin Abayomi, a madadin Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC), yayin wani taronsa da manema labarai, ya na mai cewa, matar ta shigo Nijeriya ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

NCDC ta ce, matar mai shekaru kimanin 30 a duniya, ta nuna alamomin kamuwa da cutar ne tun yandu bayan da a ka kebe ta da nufin ta kwashe kwanaki 14, kamar yadda a ka saba yi wa duk wanda a ke tsammanin ya na dauke da cutar.

To, amma hukumar ta NCDC ta ruwaito Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya na cewa, maras lafiyar na nan a cikin hayyacinta.

“Ta na cikin nutsuwa matuka gaya kuma a na cigaba da ba ta magani a Asibitin Kula da Cututtukan Masu Yaduwa da ke 20,000 ba, a sallami sauran 30,000; ashe iyakar abinda a ke bukata a dauka kenan. Legas,” in ji ministan.

Wannan sake bullar cutar ta COVID-19, wanda shi ne na uku, dai shi ne kadai ragowa ko kuma a ce koma-bayan da a ka sake samu a yunkurin dakile cutar a Nijeriya, saboda kasancewar sauran mutane biyun da a ka samu da kwayoyin cutar, tuni sun warke har an sallame su.

Bayanan hukumomi sun kuma tabbatar da cewa, wannan maras lafiyar ba ta da alaka da wadancan mutane biyu, wadanda sun hada tafiya tare. Don haka zaman kanta ta ke yi, domin ta kwaso ta ne a guri daban kenan, wato a Ingila maimakon Italiya da mutanen farko su ka taho da ita daga can.

Tuni dai ’yan Nijeriya da dama su ke kira ga gwamnati tarayya da ta dakatar da shigowa cikin kasar ta hanyar rufe tashoshin jiragen samanta a wani mataki na dakile yaduwar cutar zuwa cikin kasar.

Kwasu kasashen Afrika dai tuni su ka rufe shige da fice cikin kasar tare da haramta gudanar da manyan tarukan da zai hada dimbin jama’a waje guda, amma har yanzu Nijeriya ba ta sanar da daukar irin wadannan matakai ba.

Sai dai kuma tun daga lokacin faruwar bullar cutar a Nijeriya, hukumomin kasar su ka hana idanunsu barci wajen ganin sun dauki matakan rigakafin yaduwar cutar, musamman a Jihar Legas, wacce ita ce babbar cibiyar kasuwancin kasar, ta hanyar bude cibiyoyin hana yaduwar cutar tare da bayar da cikakkun bayanai kan halin da a ke ciki da kuma wayar da kan jama’a.

Exit mobile version