Gwamnatin Cote d’Iboire ta amince da daftarin dokar kafa bankin makamashi na Afirka, watau BAE, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin kasar, Amadou Coulibaly ya sanar a jiya Asabar bayan wani taron majalisar ministocin kasar.
Coulibaly ya kuma shaida wa manema labarai cewa, yarjejeniyar kafa bankin wacce aka sanya wa hannu a shekarar 2024, ta tanadi Dalar Amurka biliyan 5 a matsayin babban jari na farko da za a ware musamman domin samar da kudin ayyukan makamashi da ababen more rayuwa a fadin Afirka.
- Dan Gidan Ancelloti Ya Zama Sabon Kocin Botafago FC
- 2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu
Ya kara da cewa, amincewa da daftarin dokar ta nuna wani muhimmin mataki na tabbatar da dorewar samar da kudaden makamashi da kuma ikon mallakar makamashin a nahiyar.
Ana sa ran Cote d’Iboire za ta ci gajiyar tallafin da bankin makamashin na BAE zai bayar wajen aiwatar da dabarunta na cikin gida a kan sauyin makamashi da samun wadatarsa mai dorewa.
An fara batun kirkiro da bankin BAE ne tun a shekarar 2022 a karkashin kungiyar masu samar da man fetur ta Afirka, tare da hadin gwiwar bankin bunkasa fitar da kayayyaki da shigo da su na Afirka.