Umar A Hunkuyi" />

COVID-19: Akwai Tabbacin Albashin Maris, Amma Ba Tabbacin Na Gaba – Gwamnan Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce, tana da tabbacin iya biyan albashi da kudaden fensho na watan Maris ga ma’aikatan Jihar, duk da halin da ake ciki a halin yanzun dangane da barkewar cutar Coronabirus, duk kuwa da tabarbarewa da koma-bayan tattalin arzikin Duniya da ya samo asali daga barkewar cutar ta Coronabirus.

Gwamna Atiku Bagudu, ne ya bayar da wannan tabbacin a wani zaman gaggawa da masu ruwa da tsaki da ya yi a Birnin kebbi domin duba halin da tattalin arzikin Jihar zai shiga a nan gaba kadan.
Sai dai Gwamna Bagudu ya nemi masu ruwa da tsakin da su lalabo wata hanyar da za ta tallafi halin rashin tabbas da albashin ma’aikatan Jihar zai shiga a watanni na gaba, matukar dan abin da Jihar za ta rika samu a nan gaba daga asusun tarayya ya gaza kai wa matakin abin da za a iya biyan albashin ma’aikatan Jihar, inda a yanzun haka Jihar ke biyan ma’aikatanta albashin naira bilyan 1.9 a duk wata.
Gwamnan ya nuna tabbacin da yake da shi na cewa gwamnatin Jihar za ta biya dukkanin basukan ma’aikata da kuma ma’aikatan da suka yi ritaya kamar yanda ya alkawarta tun can a baya.
Daganan sai Bagudu ya sanar da masu ruwa da tsakin cewa, lallai barkewar cutar ta Coronabirus fa ya daki tattalin arzikin Duniya gami da kasar nan fiye da zaton kowa, wanda hakan ma ya sa ba ma ta iya siyar da danyan manta.
Gwamnan ya bayyana cewa halin da ake ciki abu ne da ke da matukar damuwa, saboda a yanzun haka Jihar ta dogara ne a bisa dan abin da take samu daga asusun tarayya, wanda kuma ba ta da wata babbar hanyar samun wasu kudaden shigan baccin wannan.
Tun da farko da yake jawabi, Sakataren gwamnatin Jihar, Alhaji Babale Umar Yauri, ya bayyana cewa an kira taron gaggawan ne domin a tattauna a kan matsalolin tabarbarewar tattalin arzikin Duniya, musamman a kan abin da ya shafi Nijeriya da kuma Jihar ta Kebbi.
Babbar sakatariya a ma’aikatar kasafin kudi da tsara tattalin arziki ta Jihar, Hajiya Aishatu Usman, ta yi tilawar halin da kudaden Jihar suke a ciki, tana mai cewa kudaden da Jihar ta Kebbi ke samu sun ja baya kwarai da gaske.
Ta kara da cewa, har ya zuwa lokacin da suke gabatar da wannan taron, Jihar ba ta sami kasonta daga asusun tarayya na watan Maris ba, domin har zuwa lokacin ma dai ba a raba an bai wa kowa na shi ba a duk fadin kasar nan.

Exit mobile version