Zubairu M Lawal" />

COVID – 19: Al’Ummar Nasarawa Na Yi Wa Kansu Kiyamullaili

Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya bukaci al’ummar jihar su kasance masu taka-tsan-tsan-wajen yawan mu’amala a tsakaninsu.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su daina taruruka da zai haifar da cinkoso saboda cutar Koronabairos da take kara yaduwa a cikin al’umma.
Ya ce; “idan zai yiwu a dakatar da wasu ayyukan da ke hada cinkoson jama’a wuri daya”.
Tuni Gwamnatin jihar tabi sahun sauran Jihohi wajen ba da hutun makarantu da dakatar da ayyukan ofisoshi, kuma Gwamnan ya ba da umurnin rufe ofishin shi sakamakon cutar Koronabairos, kana ya killace kansa ba domin saboda rigakafi.
Malaman kiwon lafiya sun gwada lafiyar Gwamnan, kuma da dama Ma’aikatun Gwamnatin jihar an rage zirga zirga a cikinsu. Majalisar dokokin Jihar Nasarawa ta ba da sanarwan rufe Majalisar na tsawan mako biyu.
Haka zalika Gwamnatin jihar ta tanadi wurare na taimakon gaggawa cikin Asibiti ta yadda ko da an samu masu cutar Koronabairos za a yi masu magani a lokaci.
Jama’an Jihar Nasarawa suna yiwa kansu kiyamullaili wajen kaurace wa taro mai yawan jama’a. Kuma sun kasance masu kiyaye ka’idoji da malaman kiwon lafiya ke yin bita a kai.

Exit mobile version