Khalid Idris Doya" />

Covid-19: An Kama Sojojin Da Suka Yi Wa Mata Fyade A Rwanda

Rundunar sojin Rwanda ta ce ta kama jami’anta biyar bayan wasu mazauna yankunan marasa galihu da ke babban birnin kasar Kigali sun zarge su da yi wa mata fyade a yayin da suke tilasta wa mutane bin dokar hana fita domin hana yaduwar Cobid-19.

Mazauna Nyarutarama sun shaida wa masu shigar da kara na rundunar sojin cewa sojojin sun kuma yi wa maza duka sannan suka sace musu kayayyaki.

Daya daga cikin matan ta shaida wa ‘yan jarida cewa ranar 26 ga watan Maris wani soja ya kutsa kai cikin dakinta inda ya lakada wa mijinta duka, sannan ya yi mata fyade lokacin da ta yi yunkurin hana shi dukan mijin nata.

Gwamantin kasar ta sanya dokar hana fita domin dakile yaduwar Cobid-19, amma mazauna birnin sun yi korafin cewa jami’a tsaro suna gallaza musu.

A makon jiya, an harbe mutum biyu har lahira bayan an kama su a wajen gidajensu.

‘Yan sanda sun ce mutanen biyu sun yi yunkurin kai wa jami’an tsaro hari.

Rwanda ta tabbatar da cewa mutum 84 sun kamu da cutar Cobid-19.

Exit mobile version