Daga Ahmad Fagam
Da alama dai har yanzu ba ta sauya zani ba, domin kuwa Amurka ce kasar da ta fi kowace kasa a duniya fuskantar bala’in shu’umar cutar shakewar numfashi ta COVID-19.
A bisa ga alkaluman da cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta jami’ar Johns Hopkins ta fitar a karshen makon jiya ya nuna cewa, Amurkar ita ce ke jagorantar duniya ta fuskar adadin mutanen da annobar ta kashe da kuma wadanda suka kamu da cutar mashako ta COVID-19.
Kididdigar baya bayan nan ta nuna cewa, ya zuwa ranar Asabar din da ta gabata adadin mutanen da annobar COVID-19 ta hallaka a fadin duniya ya zarce miliyan 3. Ya zuwa ranar Asabar din jimillar mutanen da cutar ta kashe a duniya ya kai 3,001,892, yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya ya zarce miliyan 140. Cibiyar nazarin kimiyya da fasahar ta tabbatar da cewa Amurka ce kasar da annobar ta fi yi wa mummunar illa, yayin da kasar ke da yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 kimanin 31,567,744, kana cutar ta hallaka Amurkawa 566,240, wato sama da kashi 22 bisa 100 na yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya, sannan sama da kashi 18 bisa 100 na yawan mutanen da cutar ta kashe a duniya. Kasashen da suka rasa rayukan al’ummarsu wanda adadin ya zarce 100,000, sun hada da India, Birtaniya, Italiya, Rasha da Faransa. A ranar 28 ga watan Satumbar 2020, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a duniya ya cika miliyan 1, sannan cutar ta hallaka mutane miliyan 2 ya zuwa ranar 15 ga watan Janairun shekarar nan ta 2021. Koda yake, dama dai tun a farkon barkewar annobar ta COVID-19 a karshen Disambar shekarar 2019 masana sun sha yiwa gwamnatin Amurka gargadi cewa rashin daukar kwararan matakan da suka dace a kan lokaci ka iya ta’azzara al’amurra game da bazuwar cutar muddin aka gaza daukar matakai mafiya dacewa. Koda a cikin wannan mako sai da mai ba da shawara ga hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Amurka Dr Antony Fauci, ya yi barazanar cewa har yanzu Amurkar tana cikin halin rashin tabbas kuma mai yiwuwa ne kasar za ta ci gaba da fuskantar hadarin hasarar dubban rayukan ’yan kasar nan da wasu watanni masu zuwa a sanadiyyar cutar ta COVID-19. (Ahmad Fagam)