Bello Hamza" />

COVID-19: Ba Cutar Masu Kudi Ba Ce Kawai, Cewar Wata Kungiya

Wasu mazauna birnin Legas sun rufe bakinsu da hanci a wani mataki na kariya daga Coronavirus Hoto: George Osodi/Bloomberg
Shugaban Kungiyar Wabes of Success Foundation, Ocholi Yusuf, ya gargadi mutanen kauyuka kan yarda babu wata cuta Coronavirus, ko kuma yarda cutar wai ta musu kudi ce kawai.
Yusuf ya bayyana haka ne yayin da yake raba sinadarin wanke hannu guda miliyan daya da kuma wayar da kan mazauna Ogbagba a karamar hukumar Ofu da ke jihar Kogi ranar Jumma’a.
Ya ce, cutar ba karya ba ce, akwai ta kuma ba cutar masu kudi ba ce kawai, kamar yadda wasu suka yarda, inda ya ce babu ruwanta da shekaru, jinsi ko yanayin rayuwar mutum.
Ya bukaci jama’a da su rika nisantar juna sannan kuma su rika kiyaye yin tsafta don kare yaduwar cutar, ya na mai cewa gwara a ce ka kauce mata da a ce kana kokarin neman maganinta.
Shugaban ya gargadin cewa cutar ya zuwa yanzu ba ta da wani magani, don haka abin zai yi muni idan aka kyaleta ta shiga kauyuka.
Ya kuma bukaci jama’a da su rika nisantar juna, ciki har da iyalansu da jama’ar unguwaninsu, sannan kuma su bi umurnin da gwamnatin jihar ta yin a cewa ma’aikata da ke da matsayi na 01 zuwa na 13 su rika aiki daga gida.
Har wala yau, ya nemi jama’an da su bi dokar hana halartar taron sama da mutum 30 a lokaci guda.
Ya kuma kara da cewa, dalilin raba sinadarin wanke hannun shi ne tallafa wa Gwamnatin Tarayya da ta jiha wajen kare yaduwar annobar Coronavirus.

Exit mobile version