Abba Ibrahim Wada" />

COVID-19: Bai Kamata A Rage Wa ‘Yan Wasa Albashi Ba – Toni Kroos

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Toni Kroos, ya bayyana cewa bai kamata a tilastawa ‘yan wasa su rage albashinsu ba wajen taimakawa a yaki cutar Coronavirus kuma yakamata a bar kowanne dan wasa yaga ta hanyar da zai iya taimakawa.

A kwanakin baya, ‘yan wasan kungiyoyin Barcelona da Atletico Madrid suka amince da rage albashinsu da kashe 70% cikin 100% domin taimakawa da kudin wajen yaki da cutar Coronabirus data addabi duniya.

Sai dai Toni Kroos, dan asalin kasar Jamus, ya bayyana cewa yakamata a bawa kowanne dan wasa cikakken albashinsa kafin da kansa yayi tunanin abinda zaiyi wajen taimakawa amma maganar a rage albashin tun kafin a bawa mutum bai kamata ba.

“Rage albashi tun kafin yazo kamar kana mayarwa da kungiyar kudi ne amma idan aka bawa kowa kudinsa sai mutum yayi tunanin hanyar da zai iya taimakawa wajen yaki da wannan cutar ina ganin hakan zaifi sauki” in ji Kroos

Ya ci gaba da cewa “Ina ganin ba dole sai ancire kudin tun daga wajen masu biya ba saboda akwai wuraren da suke bukatar taimakao sama da inda mutum yake zaune domin yanzu duniya ce take bukata ba wata kasa ba”

Tuni dai wasu daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa ta suka hada da Paul Pogba da Zlatan Ibrahimobic da Lewandowski da Messi da Ronaldo suka bayar da gudunmawarsu wajen yaki da wannan cutar wadda ta addabi duniya.

Exit mobile version