Muhammad Awwal Umar" />

COVID-19: Duk Wanda Ya Saba Dokar Gwamnati Zai Fuskanci Hukuncin Dauri

Bayan kakaba dokar ta-baci kan bullar annobar COVID-19 a Najeriya da ya kai gwamnatin Neja, bisa jagorancin Alhaji Abubakar Sani Bello. Gwamnatin ta umurci ma’aikatan jihar daga mataki na daya zuwa goma sha biyu da su daina zuwa aiki har zuwa wani lokaci da ba ayyana ba tare da sanya dokar hana zurga zurga da karfe 9:00 na safe zuwa 12:00 na dare.

Lahadin makon nan gwamnatin ta bada nasarwar sassauta dokar daga karfe biyu na rana zuwa sha biyun dare a dukkanin fadin jihar.

Sanarwar wadda jami’ar yada labaran gwamnan jihar ta Neja, Madam Mary Noel Berje, ta sanya wa hannu, ta ce daga ranar littinin din makon gwamnati ta umurci dukkanin ma’aikata daga mataki na daya zuwa mataki na goma sha biyu da su koma bakin aiki daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyun rana daga ranar littinin din makon nan.

Gwamnatin ta cigaba da cewar daga ranar littinin gwamnati ta sassauta dokar hana fita da zurga zurgan jama’a da hana shiga jihar, inda gwamnatin ta bayyana cewar dokar za ta fara aiki na hana fita da zurga zurgar jama’a daga karfe biyu zuwa karfe goman dare, inda tace duk wanda aka samu da taka wannan dokar za a ci shi tara ko kuma zaman gidan yari ko kuma ya fuskanci dukkan biyu.

Da yake bayani ga manema labarai, sakataren gwamnatin jiha kuma shugaban kwamitin yaki da yaduwar annobar COVID-19, Alhaji Ibrahim Ahmed Ibeto, yace wannan dokar ya biyo bayan yadda jama’a ke take dokar ta hanyar cigaba da taruwa waje daya da shirya taron bukukuwa wanda wannan wata hanya ce da ke baiwa annobar damar kutsawa a cikin jama’a.

A cewar sakataren gwamnatin,  yace daukar wannan matakan ya biyo bayan yadda gwamnatin jiha ke kokarin ganin ta dakile wannan annobar daga yaduwa a cikin jihar duk da cewar har zuwa yanzu ba a samu rahoto ko daya a cikin jihar ba saboda irin matakan da gwamnati ke dauka kan wannan lamari.

Alhaji Ahmed Matane yace maigirma gwamna ya dauki matakin anfani da doka ta COVID-19 ta 2020 wanda aka amince mai na samar da tsaro da kare lafiyar jama’a.

A cewarsa, gwamnatin jiha ta sassauta dokar zurga zurgar jama’a wanda ta sanya a jihar daga karfe biyu na rana zuwa karfe goma na dare wanda ya fara aiki tun ranar lahadin makon jiya, biyar ga watan Afrilun 2020.

Ya cigaba da cewar za a bude kasuwanni daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyu na rana domin baiwa jama’a damar sayen abinci da sauran kayan bukatun yau da kullun, yace amma sauran zurga zurgan jama’a a cikin gari da shigowar baki har yanzu haramtacce ne a jihar.

Sakataren ya shelanta cewar ma’aikatan jihar daga mataki na daya zuwa mataki na goma sha biyu da gwamnatin ta umurci su zauna gida saboda tsoron yaduwar annobar, daga ranar littinin shida ga watan Afrilun nan zasu koma bakin aiki daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyun rana.

Saboda haka, dukkan kananan hukumomin da ke kan iyaka da wasu jahohi, an umurci da su tabbatar sun sanya idanu wajen hana shigowar baki tare da zurga zurgar ababen hawa da ke shigowa kananan hukumomin su, sannan dukkanin wata kafa ta shigowa jihar za ta cigaba da kasancewa garkame sai ga wadanda ke ayyukan musamman.

Da yake jawo hankalin jama’a kan labaran kanzon kurege da yadawa a jihar akan cewar gwamnati ta hana kiran sallah, sakataren ya shawarci jama’a da su daina daukar irin wadannan labaran kanzon kuregen, ya kara da cewar har yanzu gwamnatin jiha ba samu rahoto ko daya na bullar COVID-19 ba a jihar.

Exit mobile version