Abdullahi Muhammad Sheka" />

Covid-19: Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa

Gwamnatin Kano

*Ta Bada Hutun Makonni Biyu Ga Ma’aikata
A kokarin da ta ke yi na kara daukar matakan gaggawa, domin dakile yaduwar cutar Coranabirus, Gwamnatin Jihar Kano ta haramta dukkanin wasu tarukan bukukuwa tare da bukatar Ma’aikatar Lura da Harkokin Yawon Bude Ido da Al’adu, da su tabbatar da kiran masu gidajen da ake gudanar da wadannan taruka da aka fi sani da ‘Ebent Center’, a fadin Jihar Kano da cewa, su dakatar da dukkanin harkokinsu har zuwa wani lokaci nan gaba, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar LEADESHIPA A YAU.

Jawabin haka, ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin wani jawabi da ya gabatar a kafafen yada labarai a ranar Litinin, wanda aka gudanar a dakin taro na Fadar Gwamnatin Jihar Kano, inda ya ce, “daga yau mun dakatar da dukkanin wuraren gudanar da taruka, wadanda ake hada dandanzon al’umma har zuwa wani lokaci a nan gaba.”
Haka zalika, Gwamnan ya umarci Ma’aikatar lura da harkokin yawon bude ido da al’adu na Jihar Kano, da su yi aiki tare da masu wadancan gidajen gudanar da tarukan bukukuwa a fadin Jihar Kano, domin dakatar da hakokinsu daga wannan lokaci, tare da tabbtar da ingancin lafiyar al’umma baki-daya. Wannan mataki ne mai tsauri, amma ya zama wajibi yin hakan domin kare lafiyar al’umma Kano, in ji shi.
Daga nan, sai Gwamnan ya jaddada aniyar kyakkyawan shirin Hukumomin bayar da agajin gaggawa ke yi na daukar matakan da suka dace, wadanda suka hada da kaddamar da kwamitin kar-ta-kwana a dukkanin kananan Hukumomin Jihar Kano 44, da kuma mazabu 484 da ke Kano. kungiyar Direbobi za su hada hannu a kokarin da ake yi na samar da kyakkyawan tsari a tashoshin mota.
Ya cigaba da cewa, “Sarakunan Garagajiya da Malaman Addini, na cikin manyan masu ruwa da tsaki a cikin wannan kokari. Don haka, yana da muhimmancin gaske su tabbtar da tuntubar wuraren ibadu, hakan na cikin kokarin da ake yi na daukar matakan dakile yaduwa wannan cutar ta Covid-19.”
Gwamna Ganduje ya kuma kara da cewa, al’umma su yi kokari wajen kaucewa duk wasu taruka da ka iya tara jama’a sama da mutane 20, domin kare lafiyarsu, iyalansu da kuma sauran al’umma baki-daya, a koda-yaushe su cigaba taimakawa wajen karbar kyawawan shawarwari daga wurin kwararru.
Ya ce, “Bayan kaddamar da wadannan matakai, akwai kuma sauran matakan da aka dauka na rufe dukkanin makarantu a fadin Jihar Kano, domin takaita taruwar al’umma, mun kafa kwakkwaran Kwamitin kar-ta-kwana karkashin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusif Gawuna.
An yi haka ne domin tabbatar da ganin an yi amfani da dukkanin abubuwan da ake bukata, wadanda za su taimaka wajen dakile yaduwar wannan cuta tare da kare lafiyar al’umma. Haka kuma, an tanadi Cibiyar lura da wadanda za a kebe bayan an same su suna dauke da wannan cuta.”
Ganduje ya bukaci al’umma da su cigaba da bin doka da oda tare da sauraron Gwamnatoci a matakin jiha da kasa baki-daya, domin magance halin da ake ciki. Haka kuma, Gwamnan ya bayyana cewa wannan wani hali ne da aka tsinci kai a ciki mai tsananin gaske, amma dukkaninmu dole mu hada hannu tare da yin aiki domin magance matsalar.
Har ila yau, Gwamnan ya bayyana cewa, Ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano ta kaddamar da tsare-tsare domin dakile wannan matsala, wadanda suka hada da gudanar da cikakken wayar da kai, binciken wadanda ake zargi da kamuwa da cutar, gudanar da bincike a dukkanin hanyoyin shigowa Kano, samar da Cibiyoyin gwaje-gwaje a lokacin da aka hangi matsalar tare samar da ingantaccen tsarin  harkokin gudanar da matsalar cutar.”
A hannu guda kuma, Gwamnatin Jihar Kanon ta bai wa Ma’aikatanta hutun makwanni biyu, domin cigaba da dakile yaduwar cutar Covid-19, wadda ta zama barazana ga kafanin duniya baki-daya. Koda-yake dai, kamar yadda sanarwar ta nuna, wannan hutu na makwanni biyu bai shafi Ma’aikatan lafiya da sauran muhimman ayyuka ba.

Exit mobile version